Skip to main content

LABARIN SOYAYYA LAILAH DA MAJNUN KASHI NA 1

LAILA MAJNUN
Waye majnun lailah? Wani mutumne da aka yi a daular banu umaiyya abisa zance mafi inganci. Sunansa shine Qais Bn Mulawwah daga kabilar Banu Amir, Qais balaraben kauyene, ya taso tare da ‘yar gidan kawunsa mai suna LAILA BNT MAHDI IBN SA’AD Amfi sanin Laila da sunan Laila Aamiriya, tare suka taso tun suna yara suna kiwon dabobi har suka girma, suka fita daga sahun yara suka kai munzalin balagha.

A Yayin da alamun nuna balaga da cikar budurci suka gama bayyana ajikin Laila sai Qais ya rude soyayyarsa gare ta, hankalinsa ya dugunzuma ya tashi. Domin a wannan lokacin ne Qais ya lura da irin kyawun dirin da Allah ya yiwa abokiyarsa Laila, a kullum soyayyar Laila sai kara tashin gwauron zabi take yi a cikin zuciyar Qais, a cikin wannan yanayi ne Qais ya shiga rera mata waqoqin soyayya kala-kala babu dare babu rana hakance tasa Mahdi mahaifin Laila ya nemi da Qais ya fito dan maganar aure, saboda nuna soyayya da kauna sai da  Qais ya bayar da raquma hamsin gidansu Laila a matsayin kudin aure.

Ana haka sai ga wani mutum da ake kira WIRD BN MUHAMMAD wani dan hamshaqin attajiri ne daga cikin ‘ya’yayen masarautar Banu Umaiyya, katsahan yayi ido hudu da Laila a wata rana a cikin wani Lambu tana kiwon dabobinta. Daga wannan rana Soyayyar Laila ta hana Wird ya yi bacci a wannan dare! Cikin yan kwanaki kadan Iyayen Wird suka sauka a gidan su Laila dan neman aurenta ga dansu Wird.
 Daga dan uwanku sir sultan sagah
Mu hadu akashi na2

Comments

Popular posts from this blog

LABARIN AMJADU DA ASADU

Kamaruzzaman na nan Ebone suna cin duniyarsu da matansa, sai Allah ya ba Badura ciki ta haifi ɗa, aka sa masa suna Amjadu. Badura ba ta yi wata guda ba da haihuwa sai Hayatunnufusi ta haifi ɗa namiji, aka sa masa suna Asadu. Suka tashi gaba daya kamar ’yan tagwaye. Da ka gan su ka ga uban, in kun tuna yadda aka bayyana muku kyawun ubansu dazu, ba lalle ba ne sa’an nan im bayyana muku siffar ’ya’yan nan. Da yaran suka yi shekara goma sha biyu, sai Kamaruzzaman ya fara koya musu sha'anin mulki. In zai kewaya ƙasa sai ya bar su gida su yi sarauta. Aka ce su riqa rabawa, in wannan ya hau gado yau, gobe ya sauka gudan ya hau. Kome suka aikata kuwa ya zartu. Ran nan Amjadu na bisa gado, sai wata makira daga cikin sadakun uban ta rubuto masa takarda. Ta ce ya kamata ya tashi tsaye, Hayatunnufusi na nan na neman magani za ta sa a kashe shi, a kashe Badura, don ɗanta ya yi sarauta. Ta ce, “Saboda haka ya kamata mu kuma mu tashi tsaye, mu riga su. Ni zan nemi guba im ba...

HADISSAN SAYYADA FADIMA R.A

HADISAI ARBA'IN 40 DAGA SARAUNIYA 'YAR LELEN MANZON ALLAH (S) SAYYADA ZAHRA (AS) 1- An ruwaito daga Fatima (AS) tace: Manzon Allah (S) ya ce mani, “Ya Fatima duk wanda yayi salati gare ki, Allah zai gafarta masa, kuma zai riskar dashi dani duk in da nike a Aljanna.” 2- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Manzon Allah (S) ya ce ma Ali (AS). “Lalle kai ya Ali da shi’arka kuna cikin Aljanna.” 3- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Lallai Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda na kasance waliyyin sa to Ali waliyyin sa ne. Duk wanda na kasance Imaminsa to Ali Imamin sa ne.” 4- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda ya mutu akan son Ahlul-bayti to ya mutu shahidi.” 5- An samo daga Ali ibn Husain (AS) ya ce, Fatima ‘yar Manzon Allah (S) wani makaho ya nemi iznin shiga wajen ta sai tai mai hijabi, sai Manzon Allah yace mata: mi ya sa ki ka yi masa hijabi al-hali baya ganin ki? sai tace ya Manzon Allah in bai ganina,...

10 GA watan shauwal labarin tausayawa

Cike nake da damuwa da dokin Kada wannan ranar ta zo domin nasan cewar daga ita ranar bazan sake kasancewa acikin farin ciki ba. Rana ce wadda bazan taba mantawa da ita a rayuwata ba,Rana ce wadda na rasa silar farin cikina,Rana ce wadda na rasa silar kasancewata a cikakken mutum,Rana ce wadda aka cutar da zuciyata. Bazan taba mantawa da wannan Rana ba. Tafiya nakeyi a yayin da wayace a kunnena,ina tafe ina nishadi kamar babu abin da ke damuna, Kadan nake jira na karaso inda nake so naje,Amman saboda da wayar da nakeyi nakasa ganin nisan wurin da zanje. Sai kawai naji an fizge wayar da nakeyi alamu sun nuna cewar ba da wadda nake wayar ba ce,sai  naji bakuwar murya ta na dokar kunnena, Bayan mun gama gaisawa sai naji ta fadamun wata magana wadda ban taba jin irinta ba "Kayi hakuri haka Allah ya qaddara" Bansan abin dake faruwa ba,naci gaba da tafiyata Amman sai na katse wayar, Daga wannan Rana kawowa yanzu Ina cikin damuwa ......... Ta hakane ya sa bazan iya ci gaba...