Skip to main content

Posts

Showing posts from February, 2020

ZUNUBAI 100

JAN HANKALI ZUNUBAI 100 DA AL'UMMA KE AIKATAWA AMMA BA SU DAUKE SU KOMAI BA (1) Daga ido a cikin sallah. (2) Yin waige acikin sallah. (3) Wuce wa gaban mai sallah. (4) Nuna musulmi da makami. (5) Zagin(yanayin) sanyi. (6) Zagin(yanayin) zafi. (7) Yin fitsari ko bayan gida. Acikin ruwa. (8) Bayan gida (kashi) a hanya. (9) Zaman hira bayan sallar isha. (10) Zagin iska. (11) Dago kan mai bin sallah kafin liman. (12) Yin rantsuwa lokacin ciniki koda kana da gaskiya. (13) Yin aski ko yanke kunba a cikin goman farko na Zulhajj. (14) Aske gemu. (15) Barin gashin baki. (16) Barin tufafi su ja kasa. (17) Yin magana yayin da liman ke huduba. (18) Cin albasa, ko tafarnuwa lokacin shiga jama’a. (19) Hassada. (20) Bincike(mara kyau). (21) Ha’inci. (22) Zalunci. (23) Zagin musulmi. (24) Cin mutuncin mutum. (25) Gulma. (26) Kin cika alkawari. (27) Alfahari. (28) Takama. (29) Zato. (30) Warewar mutum biyu(sui Magana)alhalin su ukune,batare da iziniba. (31) Cuta...

HADISSAN SAYYADA FADIMA R.A

HADISAI ARBA'IN 40 DAGA SARAUNIYA 'YAR LELEN MANZON ALLAH (S) SAYYADA ZAHRA (AS) 1- An ruwaito daga Fatima (AS) tace: Manzon Allah (S) ya ce mani, “Ya Fatima duk wanda yayi salati gare ki, Allah zai gafarta masa, kuma zai riskar dashi dani duk in da nike a Aljanna.” 2- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Manzon Allah (S) ya ce ma Ali (AS). “Lalle kai ya Ali da shi’arka kuna cikin Aljanna.” 3- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Lallai Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda na kasance waliyyin sa to Ali waliyyin sa ne. Duk wanda na kasance Imaminsa to Ali Imamin sa ne.” 4- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda ya mutu akan son Ahlul-bayti to ya mutu shahidi.” 5- An samo daga Ali ibn Husain (AS) ya ce, Fatima ‘yar Manzon Allah (S) wani makaho ya nemi iznin shiga wajen ta sai tai mai hijabi, sai Manzon Allah yace mata: mi ya sa ki ka yi masa hijabi al-hali baya ganin ki? sai tace ya Manzon Allah in bai ganina,...