- Ita kuwa Laila tuni wanda ya aureta ya dauke daga kasar Saudiyya gabaki daya zuwa kasar Iraqi. Haka itama ta rayu cikin wannan mummunan yanayi abinka da ‘ya mace mai rauni said a rashin ganin Qais ya haddasa mata ciwon zuciya .......! Daga nan ita ma ta kamu da ciwon zuciya saboda tsananin soyayyar Qais Majnun! Tana cikin wannan hali ne na rashin ganin masoyinta Allah ya karbi rayuwarta! A lokacin da Majnun yaji labarin rasuwarta sai da yaje har kasar Iraqi ya nemi inda take, da inda aka binne ta, a makabartar da aka binne laila a daidai gindin kabarinta ya tare.....! Bashi da aiki sai kuka da wakokin soyayya a gareta. Wata rana da safe sai masu wucewa suka hangoshi (Qais-Majnun) ya kifa cikinsa akan qabarinta, ko da aka zo aka duba sai aka tarar Allah ya yi masa cikawa! Haka fa Allah yake jarabtar wasu da so. Dan haka kada ku zargeni idan kukaji ina sambatu akan abin begana abin faharina abin qaunata\(-ㅂ-)/ ♥ ♥ ♥\(-ㅂ-)/ ♥ ♥ ♥\(-ㅂ-)/ ♥ ♥ ♥\(-ㅂ-)/ ♥ ♥ ♥
Daga alqalamin dan uwanku a Allah
Ishaq Ibrahim shuaibu
Sagahn bege
Sir Sultan sagah
Comments
Post a Comment