Skip to main content

Mu'uizar MANZON ALLAH saww

Kadan daga cikin mu'ujizar MANZON ALLAH sallallahu alaihi Wasallam.
Abu Hurairata r.a yace
"Na kasance mai yawan mantuwa ba na iya haddace komai sai naje wurin MANZON ALLAH saww na sanar da shi,sai ya dauki bargonsa mai albarka ya rufa mani zuwa wani lokaci sai ya yaye Mani. Ko do ya ya ye mani wannan bargo na sa tun daga wannan rana ban qara manta wani abu ba.
Hadisai da kukaji ina ta ruwaitowa ban taba rubutawa ba, ina haddace su ne acikin kaina kuma da ace duka Hadissan da na haddace zan fada to da yawa daga cikin mutane ba zasu yarda da su ba, wanda akaji ina ruwaitowa to ko rabin wanda na ji daga wurin MANZON ALLAH saww na haddace ba su yi ba".
Dan uwa MANZON ALLAH Allah kenan daya daga cikin mu'jizarsa wadda ya warkar da Abu Hurairata shugaban masu ruwaito hadissai daga bakin MANZON ALLAH saww.
Ya zama wajaibi agareka dan uwa kaso manzon Allah fiye da kowa kamar yadda Allah Ya fada acikin suratuttauba
( قُلْ إِن كَانَ آبَاؤُكُمْ وَأَبْنَاؤُكُمْ وَإِخْوَانُكُمْ وَأَزْوَاجُكُمْ وَعَشِيرَتُكُمْ وَأَمْوَالٌ اقْتَرَفْتُمُوهَا وَتِجَارَةٌ تَخْشَوْنَ كَسَادَهَا وَمَسَاكِنُ تَرْضَوْنَهَا أَحَبَّ إِلَيْكُم مِّنَ اللَّهِ وَرَسُولِهِ وَجِهَادٍ فِي سَبِيلِهِ فَتَرَبَّصُوا حَتَّىٰ يَأْتِيَ اللَّهُ بِأَمْرِهِ ۗ وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ )


Daga alqalamin Dan uwanku a Allah
Ishaq Ibrahim shuaibu
Sagahn bege /Sir Sultan sagah
Via me at www.sagahalzangee.com
Daure ka tura ko da zuwa group

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

LABARIN AMJADU DA ASADU

Kamaruzzaman na nan Ebone suna cin duniyarsu da matansa, sai Allah ya ba Badura ciki ta haifi ɗa, aka sa masa suna Amjadu. Badura ba ta yi wata guda ba da haihuwa sai Hayatunnufusi ta haifi ɗa namiji, aka sa masa suna Asadu. Suka tashi gaba daya kamar ’yan tagwaye. Da ka gan su ka ga uban, in kun tuna yadda aka bayyana muku kyawun ubansu dazu, ba lalle ba ne sa’an nan im bayyana muku siffar ’ya’yan nan. Da yaran suka yi shekara goma sha biyu, sai Kamaruzzaman ya fara koya musu sha'anin mulki. In zai kewaya ƙasa sai ya bar su gida su yi sarauta. Aka ce su riqa rabawa, in wannan ya hau gado yau, gobe ya sauka gudan ya hau. Kome suka aikata kuwa ya zartu. Ran nan Amjadu na bisa gado, sai wata makira daga cikin sadakun uban ta rubuto masa takarda. Ta ce ya kamata ya tashi tsaye, Hayatunnufusi na nan na neman magani za ta sa a kashe shi, a kashe Badura, don ɗanta ya yi sarauta. Ta ce, “Saboda haka ya kamata mu kuma mu tashi tsaye, mu riga su. Ni zan nemi guba im ba...

HADISSAN SAYYADA FADIMA R.A

HADISAI ARBA'IN 40 DAGA SARAUNIYA 'YAR LELEN MANZON ALLAH (S) SAYYADA ZAHRA (AS) 1- An ruwaito daga Fatima (AS) tace: Manzon Allah (S) ya ce mani, “Ya Fatima duk wanda yayi salati gare ki, Allah zai gafarta masa, kuma zai riskar dashi dani duk in da nike a Aljanna.” 2- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Manzon Allah (S) ya ce ma Ali (AS). “Lalle kai ya Ali da shi’arka kuna cikin Aljanna.” 3- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Lallai Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda na kasance waliyyin sa to Ali waliyyin sa ne. Duk wanda na kasance Imaminsa to Ali Imamin sa ne.” 4- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda ya mutu akan son Ahlul-bayti to ya mutu shahidi.” 5- An samo daga Ali ibn Husain (AS) ya ce, Fatima ‘yar Manzon Allah (S) wani makaho ya nemi iznin shiga wajen ta sai tai mai hijabi, sai Manzon Allah yace mata: mi ya sa ki ka yi masa hijabi al-hali baya ganin ki? sai tace ya Manzon Allah in bai ganina,...

10 GA watan shauwal labarin tausayawa

Cike nake da damuwa da dokin Kada wannan ranar ta zo domin nasan cewar daga ita ranar bazan sake kasancewa acikin farin ciki ba. Rana ce wadda bazan taba mantawa da ita a rayuwata ba,Rana ce wadda na rasa silar farin cikina,Rana ce wadda na rasa silar kasancewata a cikakken mutum,Rana ce wadda aka cutar da zuciyata. Bazan taba mantawa da wannan Rana ba. Tafiya nakeyi a yayin da wayace a kunnena,ina tafe ina nishadi kamar babu abin da ke damuna, Kadan nake jira na karaso inda nake so naje,Amman saboda da wayar da nakeyi nakasa ganin nisan wurin da zanje. Sai kawai naji an fizge wayar da nakeyi alamu sun nuna cewar ba da wadda nake wayar ba ce,sai  naji bakuwar murya ta na dokar kunnena, Bayan mun gama gaisawa sai naji ta fadamun wata magana wadda ban taba jin irinta ba "Kayi hakuri haka Allah ya qaddara" Bansan abin dake faruwa ba,naci gaba da tafiyata Amman sai na katse wayar, Daga wannan Rana kawowa yanzu Ina cikin damuwa ......... Ta hakane ya sa bazan iya ci gaba...