Skip to main content

Posts

Showing posts from 2019

LABARIN AMJADU DA ASADU

Kamaruzzaman na nan Ebone suna cin duniyarsu da matansa, sai Allah ya ba Badura ciki ta haifi ɗa, aka sa masa suna Amjadu. Badura ba ta yi wata guda ba da haihuwa sai Hayatunnufusi ta haifi ɗa namiji, aka sa masa suna Asadu. Suka tashi gaba daya kamar ’yan tagwaye. Da ka gan su ka ga uban, in kun tuna yadda aka bayyana muku kyawun ubansu dazu, ba lalle ba ne sa’an nan im bayyana muku siffar ’ya’yan nan. Da yaran suka yi shekara goma sha biyu, sai Kamaruzzaman ya fara koya musu sha'anin mulki. In zai kewaya ƙasa sai ya bar su gida su yi sarauta. Aka ce su riqa rabawa, in wannan ya hau gado yau, gobe ya sauka gudan ya hau. Kome suka aikata kuwa ya zartu. Ran nan Amjadu na bisa gado, sai wata makira daga cikin sadakun uban ta rubuto masa takarda. Ta ce ya kamata ya tashi tsaye, Hayatunnufusi na nan na neman magani za ta sa a kashe shi, a kashe Badura, don ɗanta ya yi sarauta. Ta ce, “Saboda haka ya kamata mu kuma mu tashi tsaye, mu riga su. Ni zan nemi guba im ba...

Labarin kamaruzzaman Dan sarkin shahruzzaman

LABARIN TAUSAYAWA A cikin zamanin da an yi wani Sarki a nan gabas wai shi Shahruzzaman. Ga shi da arziki, abin har ba a magana. Cikin zamaninsa an haƙiƙance ba a taba samun mai arziki irinsa ba. Abin zai ba ka tausayi in ka ji duk abin nan da Sarkin nan ya tara ba shi da mai gadonsa, sai fa ’yan’uba. Abin ya bakanta masa ciki, kullum in ya yi zaune ba ya kome sai zulumi. Yana nan ran ran sai wani tsoho ya zo gunsa, ya ce, “Abin da na ga ya fi a cikin wannan al’amari sai ka sa a tara shaihunan malaman kasan nan duka a rokam maka Maiduka.” Sarki ya ce, “Gaskiyarka, malam. Ya ko ce roqan ni in amsa maka.” Sai ya aika kasashensa daka, aka tattaro masa manyan malaman da ke can, suka taru. Sarki ya gaya musu bukatarsa. Ko wannensu ya duka ba barci har kwana arba’in. Allah maji qan bawa, kwanakin nan arba’in ba su cika ba sai da wata daga cikin matansa ta dauki ciki. Bayan kamar wata uku ciki ya bayyana, duk gari aka yi ta murna a kan wannan. Da ciki ya yi wata tara, ma...

10 GA watan shauwal labarin tausayawa

Cike nake da damuwa da dokin Kada wannan ranar ta zo domin nasan cewar daga ita ranar bazan sake kasancewa acikin farin ciki ba. Rana ce wadda bazan taba mantawa da ita a rayuwata ba,Rana ce wadda na rasa silar farin cikina,Rana ce wadda na rasa silar kasancewata a cikakken mutum,Rana ce wadda aka cutar da zuciyata. Bazan taba mantawa da wannan Rana ba. Tafiya nakeyi a yayin da wayace a kunnena,ina tafe ina nishadi kamar babu abin da ke damuna, Kadan nake jira na karaso inda nake so naje,Amman saboda da wayar da nakeyi nakasa ganin nisan wurin da zanje. Sai kawai naji an fizge wayar da nakeyi alamu sun nuna cewar ba da wadda nake wayar ba ce,sai  naji bakuwar murya ta na dokar kunnena, Bayan mun gama gaisawa sai naji ta fadamun wata magana wadda ban taba jin irinta ba "Kayi hakuri haka Allah ya qaddara" Bansan abin dake faruwa ba,naci gaba da tafiyata Amman sai na katse wayar, Daga wannan Rana kawowa yanzu Ina cikin damuwa ......... Ta hakane ya sa bazan iya ci gaba...

LABARIN SOYAYYA lailah majnun kashi na hudu

A taqaice haka majnun ya rayu cikin wannan yanayi na abin tausayi! Ita kuwa Laila tuni wanda ya aureta ya dauke daga kasar Saudiyya gabaki daya zuwa kasar Iraqi. Haka itama ta rayu cikin wannan mummunan yanayi abinka da ‘ya mace mai rauni said a rashin ganin Qais ya haddasa mata ciwon zuciya .......! Daga nan ita ma ta kamu da ciwon zuciya saboda tsananin soyayyar Qais Majnun! Tana cikin wannan hali ne na rashin ganin masoyinta Allah ya karbi rayuwarta! A lokacin da Majnun yaji labarin rasuwarta sai da yaje har kasar Iraqi ya nemi inda take, da inda aka binne ta, a makabartar da aka binne laila a daidai gindin kabarinta ya tare.....! Bashi da aiki sai kuka da wakokin soyayya a gareta. Wata rana da safe sai masu wucewa suka hangoshi (Qais-Majnun) ya kifa cikinsa akan qabarinta, ko da aka zo aka duba sai aka tarar Allah ya yi masa cikawa! Haka  fa Allah yake jarabtar wasu da so.                            ...

LABARIN SOYAYYA Laila majun kashi na ukku

Duk da cewa itama Laila tana matukar son Qais(majnun) amma kuma hakan baya hanata ta wahalar dashi, a wasu lokutanma harda yi masa wulaqanci, baya ga yin amfani da mallakeshi da tayi wajen azabtar dashi, dama haka sha’anin mata yake shi yasa majnun awani baiti yace: “Nace da wani babban malami da na gamu dashi a makka, dan Allah ka bani labarin wacce take cutar dani, azamanin da take jiji da kai (saboda ina sonta) shin hakan da take ba laifi bane?” Sai Malamin ya fadawa Qais cewa: “Wallahi da sannu azaba zata shafe ta kuma a duniya ma saita hadu da bala’I”. Dagan an Qai yace, sai na kasa mallakar idona sai da hawaye ya zubo cikin sauri ya jiqa min aljihun rigata, sai nace, Allah ya yafe mata laifinta duk da yake a duniya dan kadanne samunta. Qais ko Laila Majnun Bai gusheba a cikin wannan hali har sai da ya samu tabin hankali. Domin ya kasance idan yaga yara suna wasan kasa yakan zauna tare dasu ya taro kasa ya rinqa gina gida irin wanda yara suke yi da kasa yana cewa cikin waqa:...

LABARIN SOYAYYA Laila da majnun kashi na biyu

Ko da mahaifan wird  suka je ga mahaifin Laila saida suka ajiye masa Manyan Raquma guda dari (100) a matsayin kudin aure, wato ribi biyu akan abinda Qais ya bayar! Daga nan lissafi ya kwacewa mahaifin Laila, domin kuwa yayi irin mugun abin kunyar nan na nuna kwadayi da son abin duniya. Bayan haka ne Mahaifin Laila ya kira ‘yarsa Laila cikin daki yanai mata hudunbar cewar ga mai kudi dan masu mulki shi zai aurawa ita! Babbar Magana! Laila taki amincewa da maganar mahaifinta a karon farko, amma sai ya yi mata barazanar cewar zai yanka ta idan har bata amince da auren Wird ba!  Kwatsam sai aka wayi gari Qais ya ji gari ya dauka da kace nace din anyiwa masoyiyarsa Laila aure, da Wird. Wanne irin hali Qais zai kasance a wannan ranar? Tun daga wannan lokacin bacci yayi hijira daga idonsa, farin ciki ya gagari zuciyarsa, damuwa bakin ciki gami da bacin Rai da takaici, zubar da hawaye babu dare babu rana, suka kasance tare da Qais a matsayin abokai na din-din-din! Wa...

LABARIN SOYAYYA LAILAH DA MAJNUN KASHI NA 1

LAILA MAJNUN Waye majnun lailah? Wani mutumne da aka yi a daular banu umaiyya abisa zance mafi inganci. Sunansa shine Qais Bn Mulawwah daga kabilar Banu Amir, Qais balaraben kauyene, ya taso tare da ‘yar gidan kawunsa mai suna LAILA BNT MAHDI IBN SA’AD Amfi sanin Laila da sunan Laila Aamiriya, tare suka taso tun suna yara suna kiwon dabobi har suka girma, suka fita daga sahun yara suka kai munzalin balagha. A Yayin da alamun nuna balaga da cikar budurci suka gama bayyana ajikin Laila sai Qais ya rude soyayyarsa gare ta, hankalinsa ya dugunzuma ya tashi. Domin a wannan lokacin ne Qais ya lura da irin kyawun dirin da Allah ya yiwa abokiyarsa Laila, a kullum soyayyar Laila sai kara tashin gwauron zabi take yi a cikin zuciyar Qais, a cikin wannan yanayi ne Qais ya shiga rera mata waqoqin soyayya kala-kala babu dare babu rana hakance tasa Mahdi mahaifin Laila ya nemi da Qais ya fito dan maganar aure, saboda nuna soyayya da kauna sai da  Qais ya bayar da raquma hamsin gidansu Laila ...

Mu'uizar MANZON ALLAH saww

Kadan daga cikin mu'ujizar MANZON ALLAH sallallahu alaihi Wasallam. Abu Hurairata r.a yace "Na kasance mai yawan mantuwa ba na iya haddace komai sai naje wurin MANZON ALLAH saww na sanar da shi,sai ya dauki bargonsa mai albarka ya rufa mani zuwa wani lokaci sai ya yaye Mani. Ko do ya ya ye mani wannan bargo na sa tun daga wannan rana ban qara manta wani abu ba. Hadisai da kukaji ina ta ruwaitowa ban taba rubutawa ba, ina haddace su ne acikin kaina kuma da ace duka Hadissan da na haddace zan fada to da yawa daga cikin mutane ba zasu yarda da su ba, wanda akaji ina ruwaitowa to ko rabin wanda na ji daga wurin MANZON ALLAH saww na haddace ba su yi ba". Dan uwa MANZON ALLAH Allah kenan daya daga cikin mu'jizarsa wadda ya warkar da Abu Hurairata shugaban masu ruwaito hadissai daga bakin MANZON ALLAH saww. Ya zama wajaibi agareka dan uwa kaso manzon Allah fiye da kowa kamar yadda Allah Ya fada acikin suratuttauba ( قُلْ إِن كَانَ آبَاؤُكُمْ وَأَبْنَاؤُكُمْ وَإِخْوَان...

Falalar Akur,ani

Assalamu Alaikum ‘Yan uwa masu daraja. Hakika babu wata babbar ni’ima da Allah ya yiwa wannan al’ummah bayan ni’imar aiko da Annabi Muhammad (SAW) kamar bamu Alqur’ani mai girma. Mu rike Alqur’ani domin riko da shi alkhairi ne duniya da lahira. Allah ya saukar da Alqur’ani ta hanyar daya daga cikin Mala’iku, wato Mala’ika Jibrilu zuwa ga Annabi Muhammad (SAW). Sanadiyyar haka, sai Mala’ika Jibril ya zama mafi alkhairi, kuma mafi falala da matsayi a cikin sauran Mala’iku, saboda falalar saukar da Alqur’anin ta wajen sa shi kadai. Kuma Allah ya saukar da Alqur’ani mai girma a cikin watan Ramadan, sai watan Ramadan ya zamanto wata mafi girman alkhairi da falala a kan sauran watannin shekara baki daya. Shiyasa Allah ya shar’anta mana yin azumi a wannan watan saboda falalar saukar da alqur’ani a cikin sa. An saukar da Alqur’ani a cikin daren Lailatul Qadri, sai daren ya kasance mafi alkhairin dare a cikin sauran dararen shekara baki daya, saboda albarkacin saukar da...