Skip to main content

Posts

Showing posts from July, 2019

LABARIN AMJADU DA ASADU

Kamaruzzaman na nan Ebone suna cin duniyarsu da matansa, sai Allah ya ba Badura ciki ta haifi ɗa, aka sa masa suna Amjadu. Badura ba ta yi wata guda ba da haihuwa sai Hayatunnufusi ta haifi ɗa namiji, aka sa masa suna Asadu. Suka tashi gaba daya kamar ’yan tagwaye. Da ka gan su ka ga uban, in kun tuna yadda aka bayyana muku kyawun ubansu dazu, ba lalle ba ne sa’an nan im bayyana muku siffar ’ya’yan nan. Da yaran suka yi shekara goma sha biyu, sai Kamaruzzaman ya fara koya musu sha'anin mulki. In zai kewaya ƙasa sai ya bar su gida su yi sarauta. Aka ce su riqa rabawa, in wannan ya hau gado yau, gobe ya sauka gudan ya hau. Kome suka aikata kuwa ya zartu. Ran nan Amjadu na bisa gado, sai wata makira daga cikin sadakun uban ta rubuto masa takarda. Ta ce ya kamata ya tashi tsaye, Hayatunnufusi na nan na neman magani za ta sa a kashe shi, a kashe Badura, don ɗanta ya yi sarauta. Ta ce, “Saboda haka ya kamata mu kuma mu tashi tsaye, mu riga su. Ni zan nemi guba im ba...

Labarin kamaruzzaman Dan sarkin shahruzzaman

LABARIN TAUSAYAWA A cikin zamanin da an yi wani Sarki a nan gabas wai shi Shahruzzaman. Ga shi da arziki, abin har ba a magana. Cikin zamaninsa an haƙiƙance ba a taba samun mai arziki irinsa ba. Abin zai ba ka tausayi in ka ji duk abin nan da Sarkin nan ya tara ba shi da mai gadonsa, sai fa ’yan’uba. Abin ya bakanta masa ciki, kullum in ya yi zaune ba ya kome sai zulumi. Yana nan ran ran sai wani tsoho ya zo gunsa, ya ce, “Abin da na ga ya fi a cikin wannan al’amari sai ka sa a tara shaihunan malaman kasan nan duka a rokam maka Maiduka.” Sarki ya ce, “Gaskiyarka, malam. Ya ko ce roqan ni in amsa maka.” Sai ya aika kasashensa daka, aka tattaro masa manyan malaman da ke can, suka taru. Sarki ya gaya musu bukatarsa. Ko wannensu ya duka ba barci har kwana arba’in. Allah maji qan bawa, kwanakin nan arba’in ba su cika ba sai da wata daga cikin matansa ta dauki ciki. Bayan kamar wata uku ciki ya bayyana, duk gari aka yi ta murna a kan wannan. Da ciki ya yi wata tara, ma...