Skip to main content

LABARIN AMJADU DA ASADU

Kamaruzzaman na nan Ebone suna cin duniyarsu da matansa, sai Allah ya ba Badura ciki ta haifi ɗa, aka sa masa suna Amjadu. Badura ba ta yi wata guda ba da haihuwa sai Hayatunnufusi ta haifi ɗa namiji, aka sa masa suna Asadu. Suka tashi gaba daya kamar ’yan tagwaye. Da ka gan su ka ga uban, in kun tuna yadda aka bayyana muku kyawun ubansu dazu, ba lalle ba ne sa’an nan im bayyana muku siffar ’ya’yan nan.

Da yaran suka yi shekara goma sha biyu, sai Kamaruzzaman ya fara koya musu sha'anin mulki. In zai kewaya ƙasa sai ya bar su gida su yi sarauta. Aka ce su riqa rabawa, in wannan ya hau gado yau, gobe ya sauka gudan ya hau. Kome suka aikata kuwa ya zartu.

Ran nan Amjadu na bisa gado, sai wata makira daga cikin sadakun uban ta rubuto masa takarda. Ta ce ya kamata ya tashi tsaye, Hayatunnufusi na nan na neman magani za ta sa a kashe shi, a kashe Badura, don ɗanta ya yi sarauta. Ta ce, “Saboda haka ya kamata mu kuma mu tashi tsaye, mu riga su. Ni zan nemi guba im ba ka, mu sa cikin abincin Asadu da shi da uwarsa, in sun ci duk su mace mu huta. Kai kuwa in ka yi sarauta ka sa ni babbar jakadiyarka. Ka san fa an ce kashe macucinka kafin ya cuce ka. In kai ba ka iyawa, ka ba ni izni ni na yi kome.”

Da yaron nan ya karanta wannan takarda sai ya yi ta kuka, ya sa aka kashe tsohuwar da ta kawo ta, aka nemi dalili aka rasa, ko uwarsa bai gaya mata ba. Ya dauki takardar ya sa a aljihu. Gari na wayewa kuma Asadu ya hau gado, shi kuma sai ga takarda daga wata makulliya ta aiko wa Asadu, ya bude ya karanta sai ya tarar da daidai abin da waccan makulliya ta aiko wa Amjadu. Wai shi kuma Asadu ya yi hankali da Amjadu, suna nan suna qullawa da uwarsa za su kashe shi da Hayatunnufusi.

Shi kuma da ya karanta ya aikata yadda wansa Amjadu ya yi duka, ko junansu ba su gaya wa abin da ya faru ba, balle wani. Ashe abin da ya sa makullan nan wannan makirci hassada ce don sun ga su ba su da ’ya’ya, kuma Sarki bai kula da su ba kamar yadda ya kula da Badura da Hayatunnufusi. Su ba bayi ba, amma am mai da su kamar bayi, don ba mai fadi a ji gidan, daga Badura sai Hayatunnufusi. Suka gama kai suka aiko da takardun nan haka, wai da su niyyarsu ko wanne ya tasam ma dan’uwa. Su kuma su yi ta kara iza su, iyayen mata ba su sani ba, har su sa su yi mutuwar kasko, fada ta zama tasuDa suka ga abin da yaran nan suka aikata, suka yi tsammani in Kamaruzzaman ya dawo za su nuna masa takardun nan ne, suka ga kuwa lalle in Sarki ya ga takardun nan, ba abin da zai hana su kwana lahira ran nan. Saboda haka suka taru su biyu, suna shawarar abin da za su fadi in Sarki ya dawo, don su riga yaran nan, ko Allah ya ba su sa’a su kuɓuta. Suna shawara kullum har suka sami dabara.

Ana nan Sarki ya dawo, da saukarsa ba su bari ya ko fito waje ba sai suka iske shi, suka ce suna da magana. Ya ƙaurace, suka tsuguna suka yi ta kulla ƙarairayi. Suka kwashe abubuwan nan da suka rubuta, suka ce yaran ne suka aiko musu su taimake su. Suka ce ko wanne bai san dan’uwansa ya aiko ba. Suka ce wai bayin nan da ya ji an kashe su ne suka aiko, wai don kada su karar shi ya sa suka kashe su. Kai, makirci dai duk wanda ka sani, har wanda ba ya faduwa, matan nan suka ce duk yaran nan sun yi shi, da Sarki ba ya nan. Suka ce sun gaya masa ne, don kada abu ya rude nan gaba, a rasa abin da ya sa shi. “In kuma kana tsammani karya mu ke yi, ka kira su ɗai ɗai ka tambaye su, ko sa iya gaya maka kowa abin da ya sa ɗan’uwansa ya kashe baiwa guda. Ka san in da suna zaman lafiya, lalle kome guda ya aikata gudan ya sani. Ka ji kowa ya ce bai sani ba, ɗan’uwan bai gaya masa ba.”

Da Sarki ya ji haka ya kira yara ya tambaye su ɗai ɗai, suka kasa fadin wani abu, don ba su gaya wa juna ba. Ya tambaye su kuma dai dai abin da ya sa suka kashe bayinsa, aka rasa maganar kamawa, don ko wannensu na jin tausayin ya bayyana asirin sosai, kada Sarki ya sa a kashe matan nan. Suna ganin in sun yi haka sai a ce don ba iyayensu ba ne.

Da Sarki yaga ba su fada masa wani abin kirki ba, sai ya harzuqa, idandunan nan suka jujuye, ya tashi ba ya ko gani ya sa aka kira tsohon nan, uban Hayatunnufsi, ya kwashe al’amarin nan duk ya gaya masa. Tsohon Sarki ya harzuka, shi kuma ya ce, “Tun muna da rai ke nan, ina ga im muka mutu?” Sarki Kamaruzzaman bai tsaya neman shawara ba, sai ya kira hauni da dare, ya ce ya tafi da ’ya’yan nan nasa daji, ya sassare su duka.

Hauni da ya tsaya wani ’yan noƙe-noƙe, Sarki ya buga masa tsawa ya ce, “Don me na ajiye ka, ba sai da ka dauki alkawari ba ka saɓa mini ba na nada ka. Kome sonsu da ka ke yi, ka san na fi ka. Tun da ka ji ko na ce a kashe su, ka san kada a tona. Abin da ka ga ya koro ɓera har ya sa ya fada wuta, to, ka tabbata hakikan ya fi wutar zafi.”

Hauni ya dauki gayawa-jini-na wuce ya rataya, ya tasa yara gaba da tsakad dare, ba wanda ya san abin da a ke ciki, daga shi hauni sai fa Sarki, ya fita, suka shiga daji, suka yi ta tafiya har gari ya waye da zuwa hauni ya ce musu “Kamaruzzaman ya ce in zo in kashe ku. Amma ni ban san dalili ba. Ni ko lalle na yi alkawari ba na wuce umarnin Sarkin. Duniyan nan duk, ko Shahruzzaman ubansa ya ce in sare ina sare shi.”

Yara suka ce, “Allah ya dade da ran baba, in ka ƙi cika aikinsa, ina amfanin ajiye ka ke nan?”

Ko wanensu ya gane laifinsa wajen kashe baiwan nan ne da kwarkwaran uban ta aiko. Amma har yanzu ba wanda ya fadawa dan’uwa abin da ya sa ya kashe baiwa guda ran da ya hau gado. Hauni ya ce, “To, ku raba, wa zam fara kansa?”

Amjadu ya ce, “Sai ka fara kaina, ba ni ne babba ba?”

Asadu ya ce, “A’a, in am fara kanka wataƙila na ji tsoro in motsa, in ta kawo kaina. A dai fara kaina, don kada in yi fargaba.”

Amjadu ya ce, “Ba na iya ganin an sare ka, tun kafin a zo gareni ma bakin ciki ya kashe ni.”Suka yi ta gardama, kowa na cewa a fara kansa. Hauni yace, “ln kunƙi gaya mini wanda zam fara sarewa, sai ku tsaya ku gama bayanku kuna tsaye, ni ko in daure ku da igiya gaba daya, tun daga hannuwanku har ya zuwa kafadu don kada wani ya goce, ku sa ni in sara sau biyu. Na ko yi alkwari da Sarki ran da na sari kato, ban dauke kansa ba a fid da ni.”

Yara suka ce, “I, haka ko ya kamata a yi.” Hauni ya sa asalwayi ya ɗaure su tamau.

Amjadu ya ce, “Sai ka komo ta gabana ka fara sarawa, don kada Asadu ya ga sa’ad da za ka sara hankalinsa ya tâshi.”

Hauni ya juyo gabansa zai sara sai dokinsa ya fırgita, ko me ya gani ya barzama dawa da gudu, Allah kadai ya sani. Hauni ya yar da takobi, ya bi doki kada ya bace. Ya bar yara nan tsaye, tun safe har rana ta yl zafi ba su motsa ba.

Da suka ga bai dawo ba, suka ce, “Ya kamata mu kwance kawunammu in muna iyawa, mu dauki takobin mu bi shi ya kashe mu mu huta. Ga yunwa da qishirwa na cimmu a banza.” Suka yi ta kici-kici har suka kwance kawunansu, suka tafi kowa na gayawa dan’uwansu dalilin da ya sa ya kashe baiwa. Suka ga ashe duk al’amarin daya ne, kowa ya fidda takardar da kwarkwarar Sarki to aiko masa, suka karanta, sai suka gane makirci ne dai matan nan suka qulla musu game da Sarki. Suka kyale, ba su ce kome ba, har suka kai ga inda ya ke.

Da suka iske shi, ashe dawan da wata zakanya mai ’ya’ya, doki ya sa hauni ya haye mata ba sanannen ciki. Zakanya ta durmushe shi za ta kashe, sai ga yaran nan. Amjadu ya sa gaya-wa-jini-na- wuce, ya sare zakanyar Hauni ya ku6uta yana kaduwa.

Asadu ya ce wa Amjadu, “Ba shi takobin maza ya kashe mu, mu kuma mu huta, ni yunwa na ke ji.”

Hauni ya dube su jiki na rawa, ga zakanya tim kwance, jini ko ina face-face, ya ce, “Kai, ku rufa mini asiri, imbi ta ina in kashe ku? Ba don ku ba, ni da ko labarina a ji? ku dai ku san inda kuka nufa. Ni ko na tafi ga Sarki in ce na kashe ku.”

Amjadu ya ce, “A’a, ni sai ka kashe mu mu huta, to, ina za mu? Don me Sarki ya ajiye ka?”

Hauni ya ce, “Bari ta ku ma, daga wannan na tuba da sare mutane. Ku ƙyale ni, ni na san abin da na gani. Ku dai ku tafi, in kuna da sauran shan ruwa, to, in ko ba ku da shi, kuma wannan ba da jinina ba.”

Da yara suka yi suka yi, ya ki kashe su, sai suka fid da takardun matan nan suka ba shi, suka ce, “In ka je ka ba baba wadannan takardu, ka ce kuma da za ka kashe mu mun ce a gaya masa wanda ya ce zai riƙa kama maganar mata da gaskiya ya ko yi da na sani. Amma mun ce ya yi mana gafara.”

Hauni ya karɓi rigunansu ya tsoma cikin jinin zakanya, ya kamo dokinsa ya hau, ya tafi gari da riguna jina-jina, watau shaidar ya cika aikin Sarki.

Da Sarki ya ga haka ya yi murna, amma da hauni ya ba shi takardu ya karanta su dai dai, ya kuma gaya masa saƙon da suka yiwo, sai Sarki Kamaruzzaman ya fado daga bisa kujera ya some. Aka watsa masa ruwa ya farfade.

Ya dauƙi takardun nan ya kai wa surukinsa, shi kuma ya karanta. Aka ba iyayen yara su kuma suka gani. Aka jawo matan nan aka sa musu kiri a wuya, aka kewaya da su gari kowa ya tsine musu. Sarki ya sa aka tsire su, aka barsu nan suna haure-haure, suna bude baki har suka mace. Hauni dai bai ce ya saki yaran ba, balle a bi. Amma batun bakin cikin Sarki Kamaruzzaman da surukinsa da iyayen yaran nan, in an ce za a tona, kai kanka ba ka jin dadin labarin ba, domin bakin ciki. Abin da yafi dai sai mu rufa Ka ji labarin Kamaruzzaman da ’ya’yansa.

Amma su yaran nan da suka ga hauni ya tafi, sai su kuma suka miqa cikin daji ba su san inda za su ba. Ba su da abinci sai ’ya’yan itatuwa. ln dare ya yi su sami ice su haye su kwana bisa, da safe su tashi su mika. Suka yi ta yin haka har kwana goma sha biyar, ba su kai ga gari Ran nan suna cikin tafiya sai suka tarad da wata barewa matacciya, ba su san abin da ya kashe ta ba. Suka yi murna, suka dauka, suka sami kartajiya suka yanyanka barewan nan kamar kilishi suka shanya. Da ya bushe suka dauka suka riqa ci sannu sannu, suna gamawa da ’ya’yan itace. Suka yi ta tafiya kwanaki, sa’an nan suka isa wani gari kato. Amjadu ya ce wa Asadu, “Sai ka tsaya nan, ni in shiga in yiwo mana bara, in na ga mutanen garin na kirki ne in zo in kira ka, mu shiga mu nemi wani gida mu yi barantaka.

Asadu ya ce, ���A’a, sai dai ni in tafi, ba na iya zama nan daji ni kadai.” Amjadu ya bar shi ya tafi, ya shiga gari.

Yana shiga sai ya fara isa gidan wani mutum, ya tsaya qotar gidan yana cewa, “Masu gida, ku taimake ni da sadaka, domin kaunarku da Shugaban talikai. Masu gida, ku ji qaina, yadda Allah ya ji kanku.”

Yana cikin bara sai wani tsoho ya fito, ya ce masa, “Samari, halama kai bako ne nan ko?”

Asadu ya ce, “I, yanzu na shigo, dan’uwana na nan bayan gari, na zo in samar mana abinci ne.”

Tsoho ya nuna alamar yana jin tausayinsa, ya kama hannunsa ya ce, “Shigo ciki in sama maka abin da za ku ci, ka ji?”

Asadu ya ce, “To.” Ya bi shi yana cewa, “Allah ya karba, Annabi ya gode, Allah ya sa muna cikin cetonsa.”

Ya saurara bai ji tsohon ya ce amin ba, sai dai shiga su ke, suka wuce can quryar gida, sai ya kai shi wani daki ya kulle ya sa wata ’yarsa ta riqa kiwonsa kamar yadda a ke turke rago. Ya ce kullum ta ba shi abinci sau biyu, da safe da dare, ruwa kuma sau biyu ko wace rana.

Ashe mutumin nan wani majusi ne, har Sarkin magiro ma a ke kiransa, watau Sarkin Tsafi. Ko wace shekara ashe abin da ya ke yi ke nan, sai ya kama Musulmi in watan zuwa tsauninsu na tsafi ya tsaya. To, Musulmin nan shi ya ke yankawa ya ba gunkinsa jinin. Sauran Arna masu yanka raguna na yi, masu shanu na yi, har da masu kaji. Amma shi Sarkin tsafin sai mutum ya kan ba gunkin ko wace shekara. To, yanzu watan zuwa bautar gunkin ya kusa, shi ya sa ya sami Asadu ya ajiye don wannan bukata. Ka ji labarin Asadu.

Amma Amjadu da yayi jira har kusan rana faduwa bai ga dan’uwansa ya dawo ba, sai shi kuma ya biyo ya duba shi. Yana shigowa sai ya gamu da wani Musulmi, ya tambaye shi ko ya ga danuwansa mai kama kaza a nan inda ya fito, Mutumin ya ce a’a, bai gan shi ba. Ya ce, “Hala ku baki ne.!

Amjadu ya ce, “I.”

Mutumin nan ya ce, “O, ai ba ku san cikin garin ba, akwai wadansu Majusawa masu bautawa wuta da gumaka, in ya fada hannun daya daga cikinsu, kai da ganinsa sai wani ikon Allah. Abin da ya fi, kai ma kanka tun da ya ke magariba ta kusa, sai ka biyo ni mu je gidana ka zauna nan, kullum ka riqa shiga gari neman dan’uwanka, in Allah ya sa kuna da rabon ganawa ku gana.”

Amjadu ya ce, “To,” Ya bi shi, suka tafi gidansa. Ashe mutumin baduku ne, Amjadu ya zauna nan yana koyon dukanci. Da rana kuma ya shiga gari neman Asadu, kullum sai kuka. Asadu shi kuma can kulle kullum hakanan. Ba wanda ya san inda dan’uwansa ya ke.

Ana nan wata rana Amjadu yana yawo sai ya gamu da wata karuwa. Da ta gan shi sai ta ce ya aure ta. Shi ko ya ce a’a, shi yaro ne, ina shi ina auren karuwa? Ga shi ko na fari ma bai yi ba tukun. Karuwa ta bi shi, ta ce ita ko ina ya shiga sai ta ga gidansu. Ba ta ko son kowa sai shi, lalle kuwa ya aure ta. Amjadu ya rasa yadda zai yi da karuwan nan, ko ina ya sa kafa sai ta mai da tata nan, shi ba dama ya kai ta gidansu yana jin kunya. Saboda haka ya kwashe ta suka yi ta yawo cikin gari, su bi wannan rariya su bulla wannan. Da ma shi dabarasa, in ta gaji da ragaita ta kama gabanta ta rabu da shi, ya je gida. in ta tambaye shi ina gida, sai ya ce, “Mun kusa dai” Ka san abu ga bako, yana cikin tafiya sai ya bi wata ’yar hanya ashe ba ta bullewa, iyakarta kofar wani gida. Suka tarar gidan kulle.

Karuwar ta ce, “Gidan ke nan? Ai ko mai kyau ne, yaran naka duk sun tafi yawo ne? Na ga gida kulle.”

Amjadu ya rasa abin da zai ce, shi ba damar ya ce ba gidansa ba ne, tun da hanya ta kawo su, mutum ya taba mance hanyar gidansu? Shi ko ba ya son ya ce shi bako ne don bai san hannun wanda zai fada ba. Saboda haka ya ce, “I’ ni na aike su.”

Karuwar ta ce, “im ba su dawo ba sai mu balle marufin kofar in ga gidanka, don wata rana in dawo, ni dai im ba kai na aura ba, hankalina ba ya kwantawa.”

Amjadu ya ce, “To, mu dakata dai su taho.”

Karuwa ta tsaya jim, ba wanda ya zo, sai ta dauki dutse ta balle kyauren, ta ce, “Ni ba zama na zo ba, daga dai in ga gidanka kawai don gaba.” Sai ta kutsa kai ciki. Amjadu ya yi kamar ya ruga, ya dai kanne, ya yi kasada ya shiga, ko da ya ke bai san mai gidan ba.ba.Suna shiga sai suka tarar ga shimfidu nan anyi, ga abinci iri iri an sa bisa wani tebur, ga kujeru biyu an ajiye. Sai karuwar ta haye guda, ta bude kwanon abinci ta fara ci, tana cewa, “Ashe yaran naka aiki suka sha. Su suka dafa?”

Amjadu ya ce, “I” Ta sa ya zauna shima ya fara ci, duk gabansa na dar dar, bai san ko gidan wane ne ba ya fada. Da karuwar ta gan shi sukuku, sai ta yi masa magana, ta tambaye shi lafiya?

Ya ce, “Lafiya lau, wadansu kudi ne nawa yara suka zubar.” Suna nan sai suka ji wani tafe, Amjadu ya tashi ya tarye shi. Ashe Sarkin Fadan garin ne, wannan gidansa ne ya sa aka gina nan don shan iska. Abincin da na ce maka Amjadu sun tarar shi ya aiko da shi daga babban gidansa don yau zai zo nan shan iska.

Ko da Amjadu ya gan shi sai ya kwashe labarin karuwar duk ya gaya masa, ya ce in zai kashe shi ya kashe shi, da ma shi tun da ba ya tare da Asadu, bai kula ba ko ya mutu.

Sarkin Fada ya ce, “Ba na kashe ka. Yadda ka ce gidanka ne in na shiga ka dauke ni kamar baranka, ka yi mi ni fadan abin da ya sa na fita, ka yi ta sa ni ’yan aike-aike.”

Amjadu ya ce, “To.”

Ko da ya koma Sarkin Fada ya bi, sai ya fara masa da fada, wai don me ya tafi yawo, an ce ya share gida ya tsaya ya fita.

Sarkin Fada ya durkusa, yana ta tuba. Karuwar ta ce, “Ya fi kyau a ba shi kashi.”

Amjadu ya ce, “Gaskiyar ki, amma sai ya kara.” Suka ci gaba da cin abinci. Sarkin Fada ya debo masu ruwan wanke hannu, ya koma gefe guda, sai barci ya kwashe shi.

Ko da ganin ya yi barci sai karuwan nan ta ce sai Amjadu ya kashe shi, ita dai ta tsane shi, muddin kuwa yana nan gidan ba ta aurensa. Ta ce wai ya faye muni, kamar Amjadu kuwa ko yaron gidansa bai kamata a tarad da mummuna ba.

Amjadu ya ce shi ba ya kashe shi. Karuwa ta ce im bai kashe shi ba ita ta kashe shi. Ta tashi ta dauki takobi za ta sare shi, sai Amjadu ya kar6e takobin, ya ce ta bari, ya sare shi da kansa. Ta miqa masa, sai ya dauke kanta. Ya ta da Sarkin Fada ya gaya masa abin da ya faru duka. Sarkin Fada ya yi mamaki, ya ce sai su nade ta cikin tabarma, shi da ya ke mutumin gari ya dauka cikin daren nan, ya kai ta cikin teku ya jefa. Amjadu ya ce, “To.” Ya tashi ya taimake shi, suka nade karuwa cikin tabarma, sa’an han ya sallami Sarkin Fada, shi ko ya koma gidan da ya sauka na baduku.

Da dare ya yi Sarkin Fada ya dauki karuwa ya nufi teku. Ashe Alqalin garin na can, ya je shan iska da dare. Ko da ya ga Sarkin Fada sai ya ce, “A’a, Sarkin Fada! Ina zaka da wannan kaya cikin dare?”Sarkin Fada ya rasa abin da zai ce. Alkali ya matsa kusa, ya ce sai ya ga abin de ya dauko. Da ya ga mace ce matacciya sai ya ce, “A a a a, Sarkin Fada! Ashe har ka fara kashe mutane haka kana kwace dukiyarsu? Da ma na san arzikin nan naka ba banza ba.” Da ya tashi bai zame ba sai gidan Sarki, duk ya kwashe labarin Sarkin Fada ya gaya masa. Ko da Sarki ya ji sai ya aika aka kira Sarkin Fada, ya tambaye shi, bai yi ko musun qarya ba, don ba dama.

Da gari ya waye sai Sarki ya sa Dogarai suka bankare Sarkin Fada, aka tafi da shi kasuwa za a sare kansa. Mai yekuwa kuma ya shiga gari titi titi, yana fada wa mutane abin da Sarkin Fada ke aikatawa, da kuma yadda aka same shi, da hukuncin da Sarki ya ce a yi masa. Yana cewa ba a dauke wa kowa ba ya fito kasuwa ya gan shi don ya zama gargadi ga na baya.

Amjadu na gida yana dinkin takalmi, ya ji shela, sai ya san abin da ya faru. Ya watsad da kayan dinkin, ya rugo kasuwa, ya tarar har Sarki ya fito, an kewaye za a sare Sarkin Fada. Sai Amjadu ya kutsa ya tarad da Sarki ya fadi ya ce, “Sarkin Fada ba shi da laifi, don ba shi ya kashe ta ba, ni ke da laifi, ni za a kashe!”

Sarki ya tambaye shi labarinsa, ya kwashe duka ya fadi, har ya kawo inda ya gamu da matan nan, da yadda ya kashe ta. Da Sarki ya ji haka sai ya sa aka saki Sarkin Fada. Ya sa mutane suka watse, ya yi ta mamakin Amjadu, da kuma wannan alkawari da ya cika. Ya ce masa yana jin labarin Sarki Kamaruzzaman tuni, daga nan garin tafiyar wata biyu ne cur zuwa can, ba mugama ba cin zango. Sabo da jaruntakan nan da ya yi, da kuma labarinsu da ya ba shi tausayi, ga shi kuma dan Sarki, sai ya yi masa Wazircin garin. Dama dame ya fashe kan kaba, na da ya mutu. Sarkin Fada kuwa aka qara masa girma, don ’yancin da ya yi. Suka zauna nan da shi da Sarki da Waziri.

Sarki ya sa mutane kullum suna ta bin gari ko sa ga Asadu, ba su gan shi ba, don yana can kulle Muryar gidan Sarkin tsafi dakin awaki, ba mai zuwa wurin sai fa shi da ’yar, mai gadin yaron. Ka ji labarin Amjadu.

Amma Asadu kullum im Majusin nan ya kewayo sai ya yi masa bulala hamsin. Suna nan haka har wata uku, sa’an nan lokacin tafiya wajen tsafi ya yi, ya sa Asadu cikin akwati ya kulle, ya dauke shi ya kai bakin teku, ya sa cikin jirgi, suna shiri za su tashi sai ga manzannin Waziri, watau Amjadu, sun zo dubawa ko sa ga Asadu, don ko da ya ke shi hankalinsa kwance ne, duk da haka kullum ba ya rabuwa da kuka da aikawa ko ina ko a ga dan’uwansa. Aka duba mutane kaf, ba Asadu, suka dawo, jirgi ya miqa. Yana tafiya cikin teku, sun yi kwana uku sai iska ta tashi, igiyoyin teku suka murda, sai aka kwashe jirgi aka tafi da shi can wani babban tsibiri inda ba hanyarsa ba suka tarar wata Sarauniya ce Musulma wai ita Magiyanatu ke mulkin tsibirin.

Arnan nan sun san Sarauniyan nan Musulma ce, sabo da haka da ta tambaye su inda za su sai suka ce su masu sayad da bayi ne, sun sayad da wadanda suka kawo duka, sai guda daya. Suka fid da Asadu suka nuna, suka ce, “Amma wannan ba mu sayad da shi.”

Sarauniya ta dubi Asadu, ta ga hasken musulunci a goshinsa, ta ga kuma lalle ba dam banza ba ne. Sabo da haka ta yi ta yi su sayar mata da shi, suka ki. Sai ta dubi Asadu, ta ce, “Ka iya rubutu?”

Asadu ya ce, “I, Allah ya ba ki nasara.”

Ta sa aka kawo masa alkalami da tawwada, ya rubuta mata labarinsa duka. Da ta karanta sai hawaye suka zubo mata. Ta dubi Arnan nan, ta ce, “Na nufe ku da ku sayar mini da yaron nan, kun ki. To, kuje an kwace muku.” Masu jirgi suka je masaukinsu, suka yi bakin cikin rabuwa da Asadu. Ba su san abin da za su yi ba, ko su koma, ko su ci gaba.

Sarauniya ta ba shi abinci irin na asali ya ci har ya koshi. Suka zauna, yana ta ba ta labarinsa duka. Da magariba ta yi Sarauniya ta nuna masa dakin da zai riqa kwana, kafin ya huta ta mai da shi garinsu. Ya shiga ya kwanta. Yana nan kwance sai ya ji duk jikinsa ya yi tsami. Ka san wanda ya yi wata shida cikin daki, ya yi kwana uku cikin akwati, ba abin da ya ke so irin miqe kafa. Saboda haka ya tashi ya fita kofar gida, yana mike qafa sai ya ga wata ’yar rijiya, ya zauna gindinta ya sha iska. Abinka da gajiyayye, sai barci ya share shi. Yana nan yana barci bakin rijiya, ashe kuma Sarkin tsafi ya fito daga masaukinsu yana yawo yana ta bakin ciki, yana dube-dube ko Allah ya ba shi ko dan jariri su sace su gudu da shi, sai ga wani na barci. Bai san ko wane ne ba. Sai ya kira ’yan’uwansa suka dauke shi a hankali, suka sa cikin akwatin da suka fidda Asadu daga gare shi, suka kulle, suka haye jirginsu, suka gudu cikin daren nan.

Da Asadu ya farka ya ji shi cikin akwati kuma, sai ya yi salati. Ko da Sarkin tsafi ya ga Asadu ne sai ya yi ihu, ya ce sai shi kafiri dan kafiri, jikan kafiri. Wuta ta aure shi, ya aure ta. Ya dubi yan’uwansa, ya nuna musu Asadu ya samo, ya ce ai tun da ya yi niyyar sai ya ba gunkinsa jinin Asadu, ko ina ya shiga sai ya dawo. Ya ce shi tsafi gare shi ba haye bane gado ne. Suka haye jirginsu, suka gudu cikin daren nan.

Amma da gari ya waye sarauniya ta nemi Asadu ba ta gan shi ba. Ta tambayi masu jirgi, aka ce ai tun da dare suka mika, sai ranta ya 6aci, ta san ba makawa su suka sace shi. Sai ta yi salati, ta yi shirin yaqi ta bi su. Da ya ke jirginta ya fi nasu sauri, can zuwa rana tsaka suka hange ta tafe. Da ma ko sun koma baya ne can wajen garin da suka fito, watau inda Amjadu ke Wazirci, don su dauko hanyar daga inda suka sani. Ko da suka hangeta tafe, sai suka ji tsoron in ta ga Asadu tare da su za ta halaka su ne kaf. Sabo da haka suka kama Asadu suka tura cikin teku, wai don in ta zo ta duba ba ta gan shi ba, ba ta halaka su ba.Cikin gidi-gidin jefa shi har suka tura duk da akwatin da ya ke ciki. Allah ya ba Asadu sa’a, ya kama akwatin, iska ta yi ta tura shi da sauri. Can zuwa magariba, bai san yadda aka fara ba, sai ga shi garin da dan’uwansa Amjadu ke Wazirci. Ka san fa bai san abin da ya faru gare shi ba, balle ya nemi gidan.

Da ya ga magariba ta yi, yana tsoron kada ya shiga garin da magariba ya fada hannun wani mugun kuma, ya rude bai san ma ko wane gari ba ne. Yana nan yana shawarwari, sai ya ga ba abin da ya fi sai ya sa akwatinsa cikin wani kabari daga kaburburan da ke kusa da shi, ya shige nan ya kwana, in gari ya waye ya isa cikin gari, abin da Allah ya qaddara kuma ikonsa yafi da hakanan. Ya shige ya kwanta. Ka ji labarin Asadu.

Amma Magiyanatu da ta tarad da Arnan nan, sai ta tambaye su Asadu, suka duka suka ce, “Allah ya ba ki nasara, ai tun da kika kwace shi rabuwarmu da ganinsa ke nan. Ta ina ma za mu bi mu ganshi kuma, kin shiga da shi gidanki?” Ta sa aka bincike kayansu duka, ba a ga kowa ba. Sabo da haka ta koma gida, ta sake shiri, ta ce in aljannu suka dauke shi im mutane ne suka sace shi, muddin yana numfashi inda ya ke duka cikin duniyan nan sai fa karfinta ya qare garin nemansa. Ta shiga nema ko ina, da kanta ta shiga duniya da mutanenta. Ka ji labarin wannan Sarauniya.

Amma Asadu, da gari ya waye sai ya fito daga cikin kabarin. Yana fitowa sai ga wani dogari ya dawo daga gadi a matsayar jlrgi, don Waziri Amjadu ya sa kullum a yi ta gadi, ko wane jirgi zai wuce a yi cajinsa ko a ga Asadu.

Ko da dogari ya ga Asadu, duk ya yi baki, kamarsa ta sake da yadda Waziri ya bayyana musu, sai ya yi tsammani barawo ne. Ya buga masa tsawa, ya tambaye shi inda ya fito, tsoro ya kama shi, ya kasa iya ba da ko jawabi. Dogari bai tsaya wata-wata ba sai ya buga masa ankwa, ya aza masa akwatin nan da ya biyo shi cikin teku, yana tsammani sato shi ya yi. Ya yi macinsa zuwa gidan Sarki yaran gari suka bi suna "Biri, biri!”

Da Sarki ya fito, dogari ya nuna masa Asadu, sai ya ce a tafi da shi ofishin Waziri, ya rubuta sunansa, ya aika da shi wajen Alkali a tuhunceshi, a ji inda ya samo akwatin nan, da kuma abin da ya sa shi kwana cikin kabari da ransa.

"Ko da aka shiga da shi wajen Waziri, suka yi arba da juna, ko wannensu sai ya fadi ya some, mutane ba su san abin da ya faru ba. Aka zuba musu ruwa suka farfade. Ko da dogari ya ga haka sai ya yi wuf ya kwance ankwa.

To, yanzu fa yaya ka ke tsammani labarin farin ciki tsakanin Amjadu da Asadu? In na bar ka ma da abin da ranka ya qulla, iyakar farin cikin nan ya ma isa, ba sai na fada maka ba. Ta ishe ka ma saboda murna Sarki ma da bai gama kome da su ba sai da ya sa aka yafe wa duk ’yan sarqan garin, aka sake su. Dogarin ko ma da ya gan shi, alherin da aka yi masa, kai, abin dai sai a yi shiru!

Ana nan ana cikin wannan murna, ana goce tambura, sai aka ga qura ta taso ta toshe sararin sama, Sarki ya ce Waziri Amjadu ya je ya dubo, in yaqi ne a shirya. Ko da ya isa, aka kai shi ga sarki, sai ya tarar ashe ma ba Sarki ba ne, wata Sarauniya ce wai ita Magiyanatu, watau waccan da ta ku6utad da Asadu daga hannun Sarkin tsafi.

Da Waziri ya tambaye ta abin da ke tafe da su, Magiyanatu ta ce ta zo neman wani saurayi ne, mai kama kaza mai kama kaza, ana ce masa Asadu. In yana nan a ba ta shi ta koma, in ko kun ki, yanzu na lahira na finku jin dadi.

Waziri ya tambaye ta abin da ya sa ta ke nemansa, ta gaya masa labarin da ya gaya mata sa’ad da ta kubutad da shi. Ta ce shi ya sa ta ke so ta mai da shi garinsu. Ta dubi Waziri, ta ce, “Kai, ai ko kun yi kama. Ba don ka fi shi qiba ba ma sai in ce shi ne.”

Waziri ya yi murmushi ya ce, “Ai ni ne wansa da ya gaya miki. Shi ko yana nan gari, yau ya iso.” Sai ya wuce gaba, dimbin yaqin Magiyanatu na biye, har gari wajen Sarki. Aka gaya masa abin da ke tafe da ita. Asadu ya zo, suka rungume juna suna murna. Al’amari ya komo sabo.

Ana nan ana ta shagali kuma, can zuwa rana tsaka sai aka hangi qura ta danno gabas da yamma, sai ganguna ke tashi. Sarki ya sa Waziri Amjadu ya je ya dubo. Magiyanatu ta ce, “A dubo me? Ku bari ko wane Sarki ne ya iso. Ko da wacce ya zo ya gamu da gamonsa.”

Sarki ya ce, “A’a, a je dai a dubo.” Waziri ya koma da hammadanci. Da isa aka kai shi ga Sarki, ya fadi ya yi gaisuwa. Dawaki ga su nan bilah-addin, sai ka ce fari. Da ya tambayi Sarkin nan abin da ke tafe da shi, sai Sarki ya ce, “Ni ne Sarkin Birnin Sin, na taho neman ’yata ce wadda a ke kira Badura, tana aure da Kamaruzzaman dan Sarki Shahruzzaman. In tana nan ku ba ni ita ku huta. In kuwa kun ki, yanzu garin nan da abin da ke cikinsa duka su koma turbaya. Yau na yi shekaru da yawa ina nemanta, ban gan ta ba.”

Waziri ko da ya ji haka sai ya fashe da kuka, don ka san fa kakansa ne. Ya gaya masa shi jikansa ne, ya kwashe labari duka ya gaya masa. Suka yi ta al’ajibi, Sarki ya ce, “Na yi tsammanin haka, ko da na ganka sai na ga kun yi kama da Kamaruzzaman.” Suka shiga gari. Da mutane suka ji labarin Sarkin Sin ne, farin ciki kuma me za mu kamanta shi? Ai babu.Ana nan gari ya cika da dawaki, na Sarkin Birnin Sin ma har a tafukka a ke daure su. Sai aka hangi wata qura daga arewa. Sarki ya ce wa Waziri, “Koma, Allah ya sa yau ranar sa'a ce.” Waziri ya tafi, aka kai shi ga Sarki. Ko da suka yi arba, sai su duka suka kasa magana. Ashe ubansa ne Kamaruzzaman da tsohon Sarkin Ebone, watau uban Hayatunnafusi uwar Asadu. Da hauni ya gaya musu bai kashe su ba, shi ne suka fito nemansu. Waziri ya tashi Sarki Kamaruzzaman ya nuna masa rakumin da iyayensu mata, watau Badura da Hayatunnufusi, su ke bisa. Ba a cewa murna wannan wuri. Ya wuce gaba, suka isa gari Asadu ya ga Kamaruzzaman, ya ga Hayatunnufusi uwarsa da Badura. Sarkin Birnin Sin shi kuma ya ga ’yarsa Badura. Wayyo Allah! Murna a wannan wuri, fadl kauyanci.

Ana nan, gari ko ina kade-kade da wake-wade da tambura abin ba mai jin na wani, sai aka hangi qura ta toshe sama, duk har ta rufe rana. Aka aiki Waziri Amjadu ya dubo kuma mene ne. Sai aka tarar Sarki Shahruzzaman ne, watau kakansu Uban Kamaruzzaman, ya sami labari bai mutu ba, sun bar rigunansu cikin jini don a daina nemansu ne, shi ya sa ya biyo nemansa cikin duniya.

Da ya ga Amjadu sai ya ce, “Kai ko samari, ko ina ka fito na ki, jinina ne.”

Waziri Amjadu ya bayyana masa ko shi wane ne.’Dan tsofo ya some don murna. Suka isa gari. Kamaruzzaman ya ga ubansa Shahruzzaman. Badura da Hayantunnunfusi suka ga surukinsu. Amjadu da Asadu suka ga kakanninu. Wayyo Allah! Wohoho! Wani al’amarin ya fi gaban a bayyana, sai a yi kurum. Garin da Sarakunan duniya biyar suka taru, duk ko taron farin ciki. To, wurin mutun ya ce zai bayyana wani abu, ai ka san kifin rijiya, wanda bai san abin da a ke kira duniya ba, sai ye ce zai qaryata mutum a wofi. Ba abin da ya fi sai dai a bar kaza cikin gashinta.

Da aka yi kwana bakwai ba barci garin, ko kana son yi ma ba dama, don tambura da kade-kade da bushe-bushe. Kowa ya ga taron nan sai ya ce iyakar duniya ke nan, ba wani mahalukin da ya rage a wani wuri, duk sa taru nan.

Da ranan nan ta dawo, watau kwana bakwai ke nan yadda na fadi yanzu, sai suka taru, Shahruzzaman ya ba su labarin wahalar da ya sha wajen neman Kamaruzzaman. Sarkin Birnin Sin ya ba da labarin shi kuma abin da ya sha wurin neman Badura. Kamaruzzaman kuma da shi da surukinsa Sarkin Ebone, uban Hayatunnufusi, suka ba da labarin wahalar da su kuma suka sha gun neman Amjadu da Asadu. Sarauniya Magiyanatu ta ba da’yar wadda ta sha kan Asadu. Amjadu kuma ya ba da wadda suka sha da Asadu, da kuma abin da suka yi da karuwa, har yayi sarauta. Kowa ya yi zugudun don tausayin wahalar da suka sha. Asadu kuma da ya fara fadin abin da ya sha na wajen ukuba tun daga ran da ya rabu da Amjadu har ran da ya sake gamuwa da shi makon jiya, sai kowa cikin Sarakunan nan ya fashe da kuka don tausayi.

Sarkin garin nan ya sa Dogarawa suka kamo Sarkin Tsafi, za a tsire shi, ya yi Kalmar Shahada ya ce ya musulunta, nan take ya kone kayan tsafi, aka kyale shi, ya kama tafarkin Fiyayyen talikkai.

Da aka yi kwana bakwai ana ba da labarun aka kare, aka kara hutawa wadansu kwana bakwai, watau ashirin da daya ke nan, sai duk Sarakunan nan biyar suka nufi garin da Sarauniyan nan Magiyanatu ke mulki. Aka tara Sarakunan qasar aka yi biki, ta auri Asadu. Ta sa wani wakilin kasar, ita ko ta bi shi suka sake dungumawa qasar Shahruzzaman, aka nada kamaruzzaman Sarki maimakon ubansa da ya tsufa. Suka zauna nan da Badura da Hayatunnufusi.Aka kuma tafi Birnin Sin, aka nada Amjadu Sarki, don ka san shi ne dan Badura, watau jika ya ke ga Sarkin Birnin Sin. Aka koma Ebone, aka nada Asadu Sarki don ka ga shi huma fa ne dan Hayatunnufusi, watau ’yar Sarkin garin. Ya zauna nan da shi da matarsa Sarauniya Magiyanatu. In sun yi wata uku nan su je can su yi wata uku. Sarkin nan da Amjadu ya yi wa Wazirci shi kuma ya ba shi ’yarsa aure. Suka yi zamansu nan, duniya ta komo hannunsu. In wannan ya yi nishadi, ya shirya ya tafi garin wannan yawo.

Allahu Akbar! Duniya na inda ta ke, masu cinta kuwa nacan na murtsukarta. Ya Allah, domin alfarmar Annaibinka, ka sa ni cikin wadanda ba za su mutu ba sai sun ce duniya, im bar wa na baya abin labari.
Daga naku
Ishaq Ibrahim Shuaibu sagah

Comments

Popular posts from this blog

HADISSAN SAYYADA FADIMA R.A

HADISAI ARBA'IN 40 DAGA SARAUNIYA 'YAR LELEN MANZON ALLAH (S) SAYYADA ZAHRA (AS) 1- An ruwaito daga Fatima (AS) tace: Manzon Allah (S) ya ce mani, “Ya Fatima duk wanda yayi salati gare ki, Allah zai gafarta masa, kuma zai riskar dashi dani duk in da nike a Aljanna.” 2- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Manzon Allah (S) ya ce ma Ali (AS). “Lalle kai ya Ali da shi’arka kuna cikin Aljanna.” 3- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Lallai Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda na kasance waliyyin sa to Ali waliyyin sa ne. Duk wanda na kasance Imaminsa to Ali Imamin sa ne.” 4- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda ya mutu akan son Ahlul-bayti to ya mutu shahidi.” 5- An samo daga Ali ibn Husain (AS) ya ce, Fatima ‘yar Manzon Allah (S) wani makaho ya nemi iznin shiga wajen ta sai tai mai hijabi, sai Manzon Allah yace mata: mi ya sa ki ka yi masa hijabi al-hali baya ganin ki? sai tace ya Manzon Allah in bai ganina,...

10 GA watan shauwal labarin tausayawa

Cike nake da damuwa da dokin Kada wannan ranar ta zo domin nasan cewar daga ita ranar bazan sake kasancewa acikin farin ciki ba. Rana ce wadda bazan taba mantawa da ita a rayuwata ba,Rana ce wadda na rasa silar farin cikina,Rana ce wadda na rasa silar kasancewata a cikakken mutum,Rana ce wadda aka cutar da zuciyata. Bazan taba mantawa da wannan Rana ba. Tafiya nakeyi a yayin da wayace a kunnena,ina tafe ina nishadi kamar babu abin da ke damuna, Kadan nake jira na karaso inda nake so naje,Amman saboda da wayar da nakeyi nakasa ganin nisan wurin da zanje. Sai kawai naji an fizge wayar da nakeyi alamu sun nuna cewar ba da wadda nake wayar ba ce,sai  naji bakuwar murya ta na dokar kunnena, Bayan mun gama gaisawa sai naji ta fadamun wata magana wadda ban taba jin irinta ba "Kayi hakuri haka Allah ya qaddara" Bansan abin dake faruwa ba,naci gaba da tafiyata Amman sai na katse wayar, Daga wannan Rana kawowa yanzu Ina cikin damuwa ......... Ta hakane ya sa bazan iya ci gaba...