Ko da mahaifan wird suka je ga mahaifin Laila saida suka ajiye masa Manyan Raquma guda dari (100) a matsayin kudin aure, wato ribi biyu akan abinda Qais ya bayar!
Daga nan lissafi ya kwacewa mahaifin Laila, domin kuwa yayi irin mugun abin kunyar nan na nuna kwadayi da son abin duniya. Bayan haka ne Mahaifin Laila ya kira ‘yarsa Laila cikin daki yanai mata hudunbar cewar ga mai kudi dan masu mulki shi zai aurawa ita! Babbar Magana! Laila taki amincewa da maganar mahaifinta a karon farko, amma sai ya yi mata barazanar cewar zai yanka ta idan har bata amince da auren Wird ba!
Kwatsam sai aka wayi gari Qais ya ji gari ya dauka da kace nace din anyiwa masoyiyarsa Laila aure, da Wird. Wanne irin hali Qais zai kasance a wannan ranar? Tun daga wannan lokacin bacci yayi hijira daga idonsa, farin ciki ya gagari zuciyarsa, damuwa bakin ciki gami da bacin Rai da takaici, zubar da hawaye babu dare babu rana, suka kasance tare da Qais a matsayin abokai na din-din-din!
Wake waken soyayya sune zancensa, bashi da abokin hira sai wakar da yake yiwa laila ga kadan daga irin abinda yake cewa:
zuwa ga Allah nake kai kukan son laila
kamar yadda maraya yake kai kukan maraicinsa zuwa a Allah.
Marayanda da kafarsa ta karye gashi kuma dangi sun gujeshe
Lallai rasa iyaye abune mai girman gaske.
Haka Qais da aka yiwa lakabi da “Majnunu lailah” yake bin kwararo kwararo da saman manyan duwatsu da bakin ruwa da cikin furanni yana rerawa Laila wadannan baituka masu motsa zuciya bai gushe ba harse da akayi masa.mu hadu a kashi na ukku
Comments
Post a Comment