Duk da cewa itama Laila tana matukar son Qais(majnun) amma kuma hakan baya hanata ta wahalar dashi, a wasu lokutanma harda yi masa wulaqanci, baya ga yin amfani da mallakeshi da tayi wajen azabtar dashi, dama haka sha’anin mata yake shi yasa majnun awani baiti yace:
“Nace da wani babban malami da na gamu dashi a makka, dan Allah ka bani labarin wacce take cutar dani, azamanin da take jiji da kai (saboda ina sonta) shin hakan da take ba laifi bane?” Sai Malamin ya fadawa Qais cewa: “Wallahi da sannu azaba zata shafe ta kuma a duniya ma saita hadu da bala’I”. Dagan an Qai yace, sai na kasa mallakar idona sai da hawaye ya zubo cikin sauri ya jiqa min aljihun rigata, sai nace, Allah ya yafe mata laifinta duk da yake a duniya dan kadanne samunta.
Qais ko Laila Majnun Bai gusheba a cikin wannan hali har sai da ya samu tabin hankali. Domin ya kasance idan yaga yara suna wasan kasa yakan zauna tare dasu ya taro kasa ya rinqa gina gida irin wanda yara suke yi da kasa yana cewa cikin waqa: “abokaina kuzo kuga gidana nida laila”....!
A yayinda al-amari ya tsananta sai mutane suka baiwa mahaifin Majnun wato Qais shawara da ya daukeshi ya kaishi ka’aba (dakin Allah) ya umarce shi da ya roqi Allah ya cire masa son Laila! Amma saboda tsananin soyayya a yayin da suka je dakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa: kama tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka son Laila sai Majnun ya kama yace: “Allah na tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da nake yiwa Laila ba . . . Mu hadu a kashi na hudu na karshe

Comments
Post a Comment