HADISAI ARBA'IN 40 DAGA SARAUNIYA 'YAR LELEN MANZON ALLAH (S) SAYYADA ZAHRA (AS)
1- An ruwaito daga Fatima (AS) tace: Manzon Allah (S) ya ce mani, “Ya Fatima duk wanda yayi salati gare ki, Allah zai gafarta masa, kuma zai riskar dashi dani duk in da nike a Aljanna.”
2- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Manzon Allah (S) ya ce ma Ali (AS). “Lalle kai ya Ali da shi’arka kuna cikin Aljanna.”
3- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Lallai Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda na kasance waliyyin sa to Ali waliyyin sa ne. Duk wanda na kasance Imaminsa to Ali Imamin sa ne.”
4- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda ya mutu akan son Ahlul-bayti to ya mutu shahidi.”
5- An samo daga Ali ibn Husain (AS) ya ce, Fatima ‘yar Manzon Allah (S) wani makaho ya nemi iznin shiga wajen ta sai tai mai hijabi, sai Manzon Allah yace mata: mi ya sa ki ka yi masa hijabi al-hali baya ganin ki? sai tace ya Manzon Allah in bai ganina, ai ni ina ganin sa, sai Manzon Allah [S] yace: Lalle na shaida ke tsoka ne daga gare ni.
6- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Naji Manzon Allah (S) yana cewa, “Lalle a ranar jumma’a akwai wata sa’a babu wani mutum musulmi da zai yi muwafaka da ita yana rokon Allah ta’ala a cikin ta alhairi face ya bashi. Sai Fatima tace ya Manzon Allah wace sa’a ce wannan? Sai ya ce idan rana tana gab da faduwa.”
7- An ruwaito daga Fatima (AS) tace: Manzon Allah (S) ya ce mani, “Na aura maki wanda yafi kowa ilimi, wanda kuma shine farkon wanda ya musulunta, wanda kuma yafi kowa hakuri.”
8- An ruwaito daga Fatima (AS) tace: Manzon Allah (S) ya ce, “Duk wanda yasa zoben Akik to ba zai gushe ba yana ganin alhairi.”
9- An ruwaito daga Fatima (AS) tace: Manzon Allah (S) ya kasance idan zai shiga masallaci ya kan ce, “Allahumma igfirli zunubiy waf tahali abwaba rahmatika. Haka nan idan zai fita ya kan ce, “Allahumma igfirli zunubiy waf-tahali abwaba fadlika.”
10- An ruwaito daga Fatima (AS) tace: Manzon Allah (S) ya ce mani, “Ya masoyiyar babanta dukkan abu mai sa maye haramun ne, kuma dukkan abu mai sa maye giya ne.”
11- An ruwaito daga Fatimatuz-Zahra [AS] tace: Naji babana Manzon Allah [S] yana cewa a lokacin rashin lafiya wadda a cikin ta ya rasu, “Yaku mutane ta yiyu in rasu ba da jimawa ba, to ku saurara lalle ni na bar maku littafin Allah ta’ala da kuma Ahlu baytina. Saannan sai ya kama hannun Ali yace wannan Ali yana tare da Alkur’ani, Alkur’ani yana tare da Ali ba zasu rabu ba har sai sun same ni a tabki.”
12- An samo daga Zahara (AS) tace: Manzon Allah (S) ya shiga gare ni na shinfida shinfida ta domin yin barci, sai yace ya Fatima kada ki yi barci face kin aikata abubuwa hudu,
1-Kin sauke Alkur’ani.
2- Kin sa Annabawa su zama masu cetonki.
3- Kin yardar da muuminai.
4-Kin yi hajji da umra,
sai tace ya Manzon Allah kayi umarni da abu 4 wanda ba zan iya yin su duka ba a yanzu! sai Manzon Allah yayi murmushi, sai ya ce mata idan kika karanta kulhuwallahu sau ukku kamar kin sauke Alkur’ani, idan kin yi man salati da kuma Annabawan da suka gabace ni zamu kasance masu cetonki ranar kiyama
Idan kika yi istigfaru ga muuminai duka zasu yarda dake. Idan kika ce subhanallahi, walhamdu lillahi, wala-ilaha-illah, wallahu Akbar to kamar kin yi hajji da umra ne.”
13- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah cewa ta shiga wajen Manzon Allah sai ya shinfida mayafi sai ya ce mata ta zauna akai,saannan Hassan ya shigo sai ya ce masa: ka zauna tare da ita, saannan Husaini ya shigo sai ya ce masa ka zauna tare dasu, sa'annan Ali ya shigo sai ya ce masa ka zauna tare dasu, bayan haka sai Manzon Allah ya ce: Ya ubangiji su daga gareni ne, ni kuma daga gare sune, ya ubangiji ka yarda dasu kamar yadda ni na yarda dasu.”
14- An ruwaito daga Fatima (AS) tace: Manzon Allah (S) ya ce mani, “ kashedinki da rowa domin aibi ne wanda bai kasance wa ga mai mutunci, kuma rowa itaciya ce cikin wuta. Kuma na hore ki da kyauta domin kyauta itaciya ce daga cikin itacen aljanna.”
15- An ruwaito daga Fatima (AS) tace: Manzon Allah (S) ya ce, “Zababbunku sune wadanda suka fi ku
kyawawan Dabi’u, kuma suka fi kyautatawa matayen su.”
16- An ruwaito daga Fatima ‘yar Manzon Allah tace: Kun manta cewar Manzon Allah ranar ghadir kum ya ce, “Duk wanda na kasance shugabansa ne to Ali shugabansa ne. Da kuma cewar Manzon Allah, kai gare ni kamar matsayin Haruna da Musa ne.”
17- An ruwaito daga Fatima (AS) tace: Manzon Allah [S] ya ce, “Idan bawa yayi rashin lafiya Allah ta’ala ya kan yi wahayi zuwa ga mala’ikunsa ku dauke alkalami ga bawana matukar yana cikin rashin lafiya, domin ni na tsare shi har in karbe shi ko in kyale shi.”
A wata ruwaya na hadisin Allah zai yi wahayi ga Mala’ikunsa ku rubuta ma bawa na ladar abun da ya kasance yana aikatawa lokacin da yake da lafiya.
18- An ruwaito daga Fatima [AS] taga Manzon Allah yana kuka tace: Ya baba na in zamo fansa gare ka miya sa kake kuka? Sai ya ambata mata wasu ayoyi da Jibril ya saukar, Wa inna jahannama lamau’idum ajma’in…….
jin haka sai Fatima ta fadi tana cewa azaba sa'annan azaba ya tabbata ga duk wanda ya shiga wuta.”
19- An ruwaito daga Fatima [AS] tace lokacin da aka yi nufin kwace fadak daga gare ta: Yaku mutane shin baku ji Manzon Allah [S] ya ce, “Lalle ‘ya ta Fatima itace shugaban matayen aljanna? Su kace lalle mun ji daga Manzon Allah, sai tace to yanzu shugaban matayen Aljanna zata yi karya ta karbi abin da ba nata ba?”
20- An ruwaito daga Fatima [AS] tace: Babana ya ce, “Duk wanda yayi man sallama da kuma ke, kwana ukku to yana da Aljanna, sai aka tambaye ta shin wannan ana nufin lokacin da Manzon Allah da ke kuke raye ko har bayan rasuwar ku? Tace muna raye da kuma bayan rasuwar mu.”
21-An ruwaito daga Fatima tace Manzon Allah ya ce ma Ali, “Ya Ali lallai kai da shi’arka zaku shiga Aljanna.”
22-An ruwaito daga Fatima tace naji Manzon Allah yana cewa, “Ali shine Imami kuma Khalifa a bayana, sai jikokina Hassan da Husain da kuma Imamai tara na zuriyyar Husaini. Idan kuka bisu to zaku shiryu,in kuka saba masu to sabani zai kasance cikinku har ya zuwa ranar kiyama.”
23-An ruwaito daga Fatima tace lokacin da na haifi Husaini Manzon Allah yazo wajena bayan da ya dauke shi, sai ya miko man shi ya ce amshe shi ya Fatima lalle shi Imami ne Dan Imami kuma baban Imamai tara.”
24-An ruwaito daga Fatima ta ce, “Shi’armu sune zababbun ‘yan Aljanna.”
25-An ruwaito daga Fatima ta ce Manzon Allah ya ce, “Idan Allah yana son bawa to zai jarrabe shi da bala’oi.”
26-Manzon Allah ya ce, “Ya Fatima ki daure ma dashin zaman duniya saboda ki rabauta da ni’imar har abada.”
27-An ruwaito daga Fatima tace: Manzon Allah ya ce, “Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira to ya fadi alhairi ko yayi shiru.”
28-An ruwaito daga Fatima tace: Manzon Allah ya ce, “Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira to kada ya cutar da majwabcinsa.”
29-An ruwaito daga Fatima ta ce: Manzon Allah ya ce, “Lalle kunya tana daga cikin imani.”
30- An ruwaito daga Fatima tace: Manzon Allah ya ce, “Allah Ta’ala yana son mutum mai hakuri kuma mai kamun kai.”
31-An ruwaito daga Fatima tace, “Wanda ya fiku kusa da Allah shine wanda ya fiku kyauta.”
32-An ruwaito daga Fatima tace: Naji babana yana cewa, “Lalle Malaman shi’armu za a tada su ranar kiyama cikin kwalliya da ado na karamomi gwargodon ilimin kowannensu da kuma kokarinsu wajen ilimantar da bayin Allah.”
33-An ruwaiti daga Fatima tace, “Yin murmushi ga Dan uwanka mumini yana iya kai ka Aljanna.
34-An ruwaito daga Fatima tace: Manzon Allah ya ce, “Duk wanda aka kai ayyukansa wajen Allah tare da iklasi, to Allah Ta’ala zai biya masa muhimman bukatunsa.”
35-An ruwaito daga Fatima tace, “Abubuwa ukku da nafi so a duniya sune: Karatun Alkur’ani. Duban fuskar Manzon Allah. Infaki fisabillilah.
36-An ruwaito daga Fatima tace: Manzon Allah ya ce Mala’ika Jibrilu ya ce man, “Mai arzikin lahira shine wanda yaso Ali.”
37-An ruwaito daga Fatima tace: Manzon Allah ya shaida man cewa, “Ni ce farkon wanda zai riske shi a bayansa.”
38-An ruwaito daga Fatima tace: Naji Manzon Allah yana cewa, “Lokacin da akayi Isra’i dani zuwa sama na shiga Aljanna, sai naga a kofarta an rubuta, babu abun bautawa sai Allah, Muhammad M
anzon Allah ne, Ali shugaban mutane.”
39-Wani mutum ya ce ma matarsa cewa ta tafi wajen Sayyida Fatima ta tambayeta shin ni ina daga cikin shi’arku ko a’a? Sai taje ta tambaya,sai Sayyida Fatima tace mata,ki ce masa, “In kana aiki da umarninmu, kana kuma hanuwa da haninmu to kana cikin shi’armu,in ko ba haka to A’a.
40-An ruwaito daga Sayyida Fatima cewa tayi addu’a a rashin lafiya da tayi gabanin rasuwarta tana cewa, “Ya Ubangiji na ina rokonka albarkacin bayin ka da ka zaba, da kuma kukan ‘ya’yana saboda rabuwa dani ka gafarta ma masu zunubi cikin shi’ata da kuma shi’ar zuriyyata.”
Insha-Allah ga mai bukatar ganin sauran Hadisai da kuma littafan da aka tsamo su yana iya neman littafin "Mi’atu Ahadisu Fatimatu-Zahra".
Sai dai littafin da larabci ne aka rubuta shi saboda haka zai kasance mai fa’ida a cibiyoyi na karan
Allah ya Kara mana kaunar ahlul baiti alfarmar shugaba sallallahu alaihi wasallam
Daga Dan uwanku
Ishaq Ibrahim shuaibu sagah

Comments
Post a Comment