Cike nake da damuwa da dokin Kada wannan ranar ta zo domin nasan cewar daga ita ranar bazan sake kasancewa acikin farin ciki ba. Rana ce wadda bazan taba mantawa da ita a rayuwata ba,Rana ce wadda na rasa silar farin cikina,Rana ce wadda na rasa silar kasancewata a cikakken mutum,Rana ce wadda aka cutar da zuciyata. Bazan taba mantawa da wannan Rana ba. Tafiya nakeyi a yayin da wayace a kunnena,ina tafe ina nishadi kamar babu abin da ke damuna, Kadan nake jira na karaso inda nake so naje,Amman saboda da wayar da nakeyi nakasa ganin nisan wurin da zanje. Sai kawai naji an fizge wayar da nakeyi alamu sun nuna cewar ba da wadda nake wayar ba ce,sai naji bakuwar murya ta na dokar kunnena, Bayan mun gama gaisawa sai naji ta fadamun wata magana wadda ban taba jin irinta ba "Kayi hakuri haka Allah ya qaddara" Bansan abin dake faruwa ba,naci gaba da tafiyata Amman sai na katse wayar, Daga wannan Rana kawowa yanzu Ina cikin damuwa ......... Ta hakane ya sa bazan iya ci gaba...
Na bude wannan blog din ne domin amfanar da al umma tare da farantawa juna da kuma nishadantarwa da wa azatarwa Ina roko ga duk Wanda ya karanta wani Abu Wanda ya faranta masa rai da ya yiwa shugaba annabin rahama salati Idan kuma ka karanta wani Abu sabanin abin da na rubuta kaji bakaji dadinsaba to kayi min uziri domin ni ajizine kowa da iri na sa kuskuren Allah ya bani ikon farantawa duk Wanda ya halarci wannan sashe daga qarshe Ina cewa وبالله توفيق