LABARIN TAUSAYAWA
A cikin zamanin da an yi wani Sarki a nan gabas wai shi Shahruzzaman. Ga shi da arziki, abin har ba a magana. Cikin zamaninsa an haƙiƙance ba a taba samun mai arziki irinsa ba. Abin zai ba ka tausayi in ka ji duk abin nan da Sarkin nan ya tara ba shi da mai gadonsa, sai fa ’yan’uba.
Abin ya bakanta masa ciki, kullum in ya yi zaune ba ya kome sai zulumi. Yana nan ran ran sai wani tsoho ya zo gunsa, ya ce, “Abin da na ga ya fi a cikin wannan al’amari sai ka sa a tara shaihunan malaman kasan nan duka a rokam maka Maiduka.”
Sarki ya ce, “Gaskiyarka, malam. Ya ko ce roqan ni in amsa maka.” Sai ya aika kasashensa daka, aka tattaro masa manyan malaman da ke can, suka taru. Sarki ya gaya musu bukatarsa. Ko wannensu ya duka ba barci har kwana arba’in.
Allah maji qan bawa, kwanakin nan arba’in ba su cika ba sai da wata daga cikin matansa ta dauki ciki. Bayan kamar wata uku ciki ya bayyana, duk gari aka yi ta murna a kan wannan.
Da ciki ya yi wata tara, matan nan ta haifi da namiji wanda sa’ad da aka haife shi don tsananin kyawunsa mutane na tsegumin ko ba mutum ba ne, aljani ne. Da ya cika kwana bakwai aka sa masa suna kamaruzzaman. Ba mai iya bayyana farin cikin Sarki bisa ga wannan.
Yaro yana nan yana ta girma, har ya sami kamar Shekara goma sha biyu. Da ubansa ya ga ya yi girma haka ya ce zai yi masa aure, shi ko ya yi murabus, ya nada dan tun yana da rai.
Kamaruzzaman ya ce, “Sarauta dai ya nyi, amma aure har abada.” Uban ya yi biris da maganan nan, sai da aka yi kamar shekara guda kuma ya tabi dan da maganar aure. Yaro ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ai na gaya maka ni da aure faufau.”
Da Sarki ya ga abin da gaske ne yaron ya ke yi, sai ya kira Wazirinsa ya gaya masa abin da ya ke ciki da yaro. Ya shawarce shi dabarar da za su yi su ciwo kansa.
Waziri ya ce, “Ba yadda za a yi sai in Hakimai da Sarakuna da Alkalan kasan nan duka sun taru da Salla, a kira shi cikin taro a tambaye shi. Na san cikin wadannan ba ya musaya mana ba.“ Sarki ya ce, “To, shi ke nan, sai mun gani.” Da aka taru da Salla, Sarakunansa suka taru suka tafi gaida Sarki, sai Sarki ya kira Kamaruzzaman ya tayar masa da wannan magana.
Kamaruzzaman ya duqad da kai, ya ce, “Allah ya ba ka nasara, tun bara waccan ka ke tambayata, na ce maka ba na yin aure har im mutu.”
Sarki ya husata, don yaro ya ba shi kunya cikin taro. Sai ya sa dogarawa suka kama shi, aka kai shi wani tsohon gida can kusa da wani rafi, aka tsare. Da mutane suka tashi, Sarki ya dubi Waziri, ya ce, “Tsohon banza! Ka ba ni 6atattar shawara, ka sa dana ya ba ni kunya a cikin taro. To, sai ka fadi abin da kuma ka ga ya fi a yi masa, mu ji.”
Waziri ya ce, “Allah ya huci zuciyarka, sai a bar shi can bakin kogin nan mu gani, ko ya ji tsoro ya amsa shawararmu.”
Sarki ya ce, “To.” Aka bar yaro can tsare kwana da kwanaki, ba mai zuwa wajensa, shi ba a barinsa ya zo wurin wani. Sai bayan kwana bakwai Sarki kanzo da shi da Wazıri su tambaye shi ya yarda a yi masa aure? In ya ce har abada ba ya aure, sai su fuce. Ka ji labarin Kamaruzzaman.
To, ashe kuma a can qasar Sin akwai wata yarinya ’yar wani babban Sarki na Gayur, an yi an yi ita kuma ta yi aure, ta ce ba ta yi. Sunan wannan ’yar Sarkin Badura. A wajen Birnin Sin kuwa, tun da a ke ganin kyakkyawa ba a ta6a ganin kamar Badura ba.
Suka ta da Kamaruzzaman. Da ya farka ya ji mutum bayansa, ya duba sai ya ga yarinya wadda ba irinta nan duniya, ya ce a ransa, “Da wannan za a aura mini da na yarda.” Ya yi kamar ya ta da ita, ya ji tsoron ko an kawo ta ne don ta dauke hankalinsa. Saboda haka ya kanne, ya hade begensa. Aljannu suka sa ya yi barci. Ka san fa ko da ya ke suna kallonsa, shi ba shi da ikon ganinsu.
Da ya yi barci, suka ta da Badura su ga abin da ita kuma za ta yi. Da farkawarta ta ga Kamaruzzaman, sai ta ce, “A a a a! In dai wannan baba ya ke so ya aurad da ni ga shi, na yarda.” Ta fa kafa masa ido ba ta ko kiftawa, sai ta zare zoben hannunta ta sa masa, ta zare nasa ta sa hannunta. Sai aljannun suka sa ta yi barci. Suka dauke ta, suka mayar da ita Birnin Sin. Sauran aljannun nan suka ce wa Maimuna Kamaruzzaman ya fi kyau, don suna tsoron kada ta yi fushi da su. Ka ji inda wannan ta kwashe.
To, da gari ya waye sai Kamaruzzaman ya ce wa bawan da ke tsaronsa, “Shin yarinyar da Sarki ya sa ta zo nan wurina jiya da dare ’yar wane Sarki ce? In dai ita ce da ma a ke so in aura, to, ka gaya masa na yarda na yi aure.”
Bawa ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ai ba a kawo wata nan ba jiya da dare.-”
Kamaruzzaman ya ce, “Kar ka yi zancen banza. lna wasa da kai ne? Ka tafi ka ce wa Sarki ina sonta.”
Bawa ya tsaya cif shi bai ga yarinya ba. Da Kamaruzzaman ya yi fushi sai ya kama gemun bawan nan, ya yi ta dukansa, wai sai ya gaya masa gaskiya. Bawa da ya ji za a halaka shi sai ya ce', “Na san maganar, da ma an kawo ta a gani ne ko ka ce kana so."
Kamaruzzaman ya ce, “Waddare gulya'e! Da da girma da arziki an ce ka fadi, ka tsaya yi mini wadansu Qusurwoyi.” Ko da bawan ya samu ya kubuta, da ya garzaya bai zame ba sai gaban Sarki, ya kwashe labarin dansa duk ya fada masa.
Da Sarki ya ji haka sai ya bushe da dariya, yana tsammani ya kusa biyuwa ne. Ya aike Waziri ya je ya jiwo. Da Waziri ya isa sai Kamaruzzaman ya ce masa, “Yarinyar da kuka kawo mini jiya in ita za a nemam mini, to, na yi aure, amma im ba ita ba ce, ba na yi.”
Ka san wannan al’amarin ba wanda ya san an yi shi, daga yaran nan biyu sai fa aljannin nan. Saboda haka Waziri ya ce ba su san wannan magana ba. Kamaruzzaman ya rarrashe shi, Waziri ya yi ta rantse-rantse ba a kawo wata yarinya ba. Sai Kamaruzzaman ya hau masa da duka. Waziri ya kwace da kyar, ya ruga buza- buza har wajen Sarki, ya kwashe abin da ya auku duka ya faddi, ya ce, “Lalle dai aljannu suka ta6a shi jiya.”
Sarki ya dubi shi, ya ce, “Kai, tsohon banza! Kai ka sa na daure shi can, to, ka tabbata in wani abu ya same shi ka kuka da kanka.” Ya tashi ya nufi gidan da kansa, Waziri na biye. Da isarsu yaro ya tashi ya gai da uban da harshe mai dadi. Sarki ya amsa, sa’an nan ya dube shi, ya ce, “Wace yarinya ka gani ne na ke jin wai ka ce kana sonta?”
Kamaruzzaman ya duqad da kai don kunya, ya ce, “Wadda kuka kawo mini jiya, har kuka sa ta sauya zobenta da nawa, ga shi. Ba na son wata magana a neman mini ita, na aura.”
Sarki ya ce, “Wallahi mu ba mu kawo maka wata ba. Ko kuwa aljannu ke son taba ka ne? Bari mu gani. Yau wace rana ce?”
Kamaruzzaman ya ce, “Lahadi, gobe Litinin, sai Talata, Laraba, Alhamis. Aljumma’a, Asabar, ko ba su ba ne?”
Uban ya ce, “Hakanan ne fa, ashe kana da sauran hankali, amma ba mu kawo kowa nan ba."
Kamaruzzaman ya ce, “Na ce naa aure ta, to, mene ne kuma na qin amsa mini? Yaya za ku ce ba ku kawo kowa ba? Ga ko zobe, kowa ya san ba nawa ba ne. An ta6a ganin inda mutum ya yi mafarki yana yaqi, ya tashi ya gan shi da takobi a hannu?”
Hankalin Sarki fa duk ya dugunzuma da ya ga yaro ya rude. Aka sa malamai da bokaye su yi ta kawo masa maganin aljannu. Duk a banza. Kullum Sarki sai laifin Waziri ya ke gani, ya ce wai shi ya ba da dabarar, Kamaruzzaman wasa-wasa abu ya koma ka mar ciwo, ba ya ci ba ya sha kwana da kwanaki, sai da kyar a dura masa kunu. Ka san soyayya babbar abu ce. Ka ji abin da ya faru ga Kamaruzzaman.
Amma abin da ya faru ga Badura ya ba Yu mamaki in kun ji, duk daya ne da abin da ya faru ga yaron nan , Ita kuma ta kwanta ba ci ba sha, ana nemo malamai da bokaye suna ba ta maganin aljannu.
Na gaya maka inda aka tsare Kamaruzzamaiı da ma kusa da kogi ne. To, tun da yaron nari ya rude haka zaman fadanci ya koma a zauren gidan. Ran nan ana zaune sai aka hango wani mutum kogin nan ya ciwo shi. Aka tashi aka fada aka dauko shi, aka matsa cikin, ruwa ya yi ta fita. Aka jiyyace shi, bayan kamar kwana uku ya warke.
To, ashe shi falke ne, ba inda ba ya bugawa, har Birnin Sin ya tafi. Yanzu ma daga wajajen can ya fito. Ya ko baro Badura ’yar Sarkin Sin tana ciwon wani yaron da ta gani da dare, har ta musaya zobe da nasa. to da kuma ya zo nan ya ji abin da Kamaruzzaman ke ciki, ya ji kuma labarin abin da ya auku gare shi kamar na Badura ne, sai ya ce a ransa, “Watakila yaran nan aljannu suka gama su. Watakila wannan shi ne wanda Badura ke so. Amma bari in gani. ln na ga kyaunsa ya dace da Badura ta yi begensa haka, na yi sa’ar fatauci.” Aka kai shi ga Kamaruzzaman. Ko da ya gan shi sai ya ce, “Ba shakka wannan shi ne.” Ya dubi Sarki, ya ce yana da magani, amma sai a watse a ba su wuri su biyu.
Sarki ya ce, “ln ko ka warkad da shi, zan yi maka kyauta wadda za ta ishe ka zaman duniya har ’ya’yanka.”
Falke ya ce, “To, madalla.” Ya shiga daki ya tarad da Kamaruzzaman, ya ce, “Albishirinka.”
Kamaruzzaman ya ce, “Goro.”
Falke ya ce, “Bukatarka ta biya.” Ya kwashe labarin Badura duk har da siffarta ya gaya wa Kamaruzzaman. Koda Kamaruzzaman ya ji ya ba da siffarta daidai da yadda ya ganta da dare, sai ya yi wuf ya tashi, ya rungume falke yana cewa. “To, yaya za mu yi mu sadu da Birnin Sin gobe?
Falke ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ai daga nan zuwa Birnin Sin tafiyar wata duniya ce. Abin da dai ya fi yanzu sai ka ce ka warke. Amma kada ka gaya wa kowa abin da mu ke ciki. Im mun yi kamar wata guda sai ka ce mu je kilisa. Ka sami jaka ko biyar ka kai mana wani wuri ka 6oye don guzuri. Daga wajen shan iska sai mu wuce. Ka san im ba haka ba Sarki ba zai bari ku rabu ba.” Kamaruzzaman ya ce, “Hakanan ne.”
Falke ya kira Sarki, ya ce, “Kamaruzzaman ya warke, da ma aljannu ne suka ta6ashi, na ko yi masa addu’a.”
Batun murna da aka yi a wannan rana sai ya yi qurum. Ta ishe ka ma har tambura aka buga, hankalin kowa ya kwanta, tun ba Waziri da da za a daure ba. Alherin kuwa da wannan falke ya samu, ka san wannan ba sai am fadi ba. Ana nan ana nan, bayan kamar wata guda sai kamaruzzaman ya yi yadda falken nan ya shawarce shi, suka dunguma. Da suka shiga daji sai suka sami awakin wadansu Filani suka saya, suka yanka, suka zubad da jinin ko ina. Kamaruzzaman ya jefa rigarsa cikin jinin, farke kuma ya yi hakanan. Dabararsu don in an zo nemansu aka ga wannan sai hankali ya kwanta, a dangana. Su kuwa suka hau dawaki, suka yi ta yi. Falke shi ne aboki, shi ne bara. Ka ji abin da ya faru ga Kamaruzzaman.
Amma Shahruzzaman da la’asar ta yi ba a ga sun dawo ba sai aka hau dawaki aka bi. Aka yi nema har dare ba a gan su ba, aka komo. Da safe kuma Sarki ya ce a koma, kada kowa kuwa ya sake dawowa sai an ga inda Kamaruzzaman ya ke. In ko ba su gan shi ba. su yi ta bin duniya har su mutu duka can garin nema.Badura kuwa, ko da ta tashi da asalatun fari ta nemi miji ba ta gani ba, sai al’amarin aljannu ya fado mata a rai, don ta tuna abin da ya auku gare su da fari. Ta tashi tana kewaya wurin, sai ta kai gindin tsamiyan nan ta ga buta a yashe, sai ta dawo ta hakikance aljannu suka dauke shi. Ta rasa abin da za ta yi. Ita ba abin ta korna ba ta bar shi, ita ba abin ta ci gaba ba, to, ta ce me? Sai ta koma ta sake dabara. Ka san da ma sun yi kama, sai ta yi shiri irin nasa, ta hau raquminsa, ta yi wa wata baiwa shiri irin nata, ta sa ta yi lullu6i yadda ta kan yi, ta hau raquminta. Suka yi ta tafiya, ban da su biyu ba wanda ya san abin da ya faru. To, dabarar Badura su isa Birnin Ebone inda za ta sa a riqa duba Kamaruzzaman a boye har ta sami labarinsa.
Da Badura ta sauka garin, sai ta tarar ashe Sarkin garin kuma na da wata ’yarsa wadda a ke kira Hayatunnufusi, ba shi da wani da ba jika, sai wannan yarinyar ita kadai. Duk nan qasarsu ita kuma ba a ta6a ganin wanda ya kai ta kyau ba.
Na gaya maka Ba’dura fa da shiri irin na maza ta ke, har da nadi da amawali. Ko da bayin Sarkin Ebone suka kawo wa Badura abinci, suka ga kyaunta, sai suka je suka tsegunta wa Hayatunnufusi, wata tsohuwa ta la6a6o da ita ta zo ta ga Badura. Sai yarinya ta ce ita ba ta son kowa sai baqon dan Sarkin nan, watau Badura. Ba su sani ba mace ce.
Da Sarki ya tambayi wani bawa sunan ubangijin nan nasu sai ya ce, “Kamaruzzaman dan Sarki Shahruzzaman. Matarsa kuwa, wadda ba ta ko yarda a ga fuskarta don kunya, ’yar Sarkin Birnin Sin ce.”
Akalallabi Badura da ta aurı Hayatunnufusi, ta ga ba damar ta ce a’a, sai ta yarda. Aka yi aure, aka yi shagali mai yawa. Ba a san mace ce ta auri mace ba.
Da aka natsa, Badura ta lura da Hayatunnufusi ta ga ta kirki ce, sai ta ce mata, "Rantse yanzu, in na gaya miki labarina duka, za ki taimake ni, ba ki tona mini asiri ba.”
Hayatunnufusi ta rantse, sa’an nan Badura ta kwashe labarinta kaf ta gaya wa Hayatunnufusı. Da yarinya ta ji haka, sai ta fashe da kuka don tausayi, ta ce, “To, in Allah ya so ba mai jin wannan. In Allah ya nufa ya dawo, ko an sami labarinsa, in ya so shi ya aure ni mu tafi tare. Ni dai yanzu ba na iya rabuwa da ke, don mun saba, kome munin halin mijinki kuwa na aure shi, ko don ke.” Suka rufa wa kansu asiri, suka yi ta zama. Badura kullum taje fada ta harde a kan karaga kamar namiji. Da Sarkin Ebone ya ga hankalin Badura ya kwanta da ’yarsa, sai ya yi murabus, aka nada Badura sarauta. Mace da mata biyu ga shi kuma tana sarauta, amma ba a sani mace ce ba. Ka ji labarin Badura.
Amma Kamaruzzaman kullum yana nan yana ta aiki a lambun har ya iya jan cakarkara. Bayan kamar wata biyu sai ga jirgi ya zo. Mai lambu ya sami kwando ya cika wa Kamaruzzaman da kayan marmari, su haure da gwanda da sauran irin kayan lambu. Kamaruzzaman ya dauki zoben Badura, watau wanda aljannu suka yi masa musaya, ya sa qarkashin kwandon nan, ya mai da kayan lambun nan bisa. Abin da ya sa ba ya sa zoben a hannu yanzu, don ya rame kwarai saboda wahala da bege, har zoben ba ya zama a hannunsa, sai ya riqa sullewa yana faduwa. Don gudun kada ya fadi ya 6ace, shi ya sa da riqa ajiye shi cikin kaya.
To, ko da mai lambu ya tafi da Kamaruzzaman aka yi jingar abin da za a biya zuwa babban Birnin Ebone, domin nan ne matsayar jirgin, watau fa inda Badura matarsa ke Sarauta. Mai lambu ya biya kudin sufurin Kamaruzzaman, ya sa kayansa cikin jirgi. Ya koma su yi sallama da mai lambu. Ashe masu jirgi sun yi gajin haquri. Da suka ga bai dawo ba da wuri, suka tuqa suka tafi da kayan Kamaruzzaman cikin jirgi. Ga su nan bayan kwana uku suka isa Birnin Ebone. Ka ji yadda wadannan tasu ta kwashe.
Kamaruzzaman kuwa da suka gama sallama da tsoho, ya rako shi wajen jirgi yana kuka, sai suka hangi jirgi ya shige teku. Suka yi kuwwar kira. Af! Ba wanda ya ji. Aka bar Kamaruzzaman nan yana bakin ciki, abin har ba ya faduwa. Babban abin da ya sa shi bakin ciki, rabuwa da zoben nan na Badura. Da shi ya kan gani ya tuna da ita, Hankalinsa ya kwanta. Ka ji aikin kaddara.
Mai jirgi kuwa da isa Ebone sai ga bayi, Sarki Badura ta aiko a tambayar mata ko akwai kayan marmari. Da ma wannan jirgi abin da ya kan sa ya je tsibirin nan ke nan don ya dauko su.
Da aka tambayi masu jirgi suka ce ai duk an sayar, saura kwando guda na wani da ya sa, amma ya makara sun bar shi. Bayi suka sayi kwandon guda, aka kai wa Badura. Ko da aka je za a sake, sai ga zobenta. Da kyalla ido ta ganshi, sai gabanta ya fadi, ta yi wuf ta dauka, ta duba, sai ta sallami bayi. Ta nuna wa matarta Hayatunnufusi ta ce, “Albishirinki!”
Hayatunnufusi ta ce, “Goro."
Badura ta ce, “Kin ga zoben nan na mijina ne.” Nan da nan aka aika dogarai suka zo da mai jirgi. Sarki Badura ta tambaye shi mai wannan kaya da ta saya.
Mai jirgi ya kwashe yadda aka yi har ya bar shi a tsibirin nan ya fadi. Sarki Badura ta ce ya koma yanzu ya zo da shi. Mai jirgi ya tashi jiki na 6ari, ya tuqa jirgi har ya isa tsibirin nan ya tarad da mai lambu, ya ce masa, “Yaron nan kyakkyawa ashe kyaun banza gare shi, 6arawo ne. An ce yanzu in tafi da shi.”
Nan da nan Kamaruzzaman ya yi sallama da mai lambu, ya kuma sake ba shi wadansu kayan marmari, suka tuko ba ko tsayawa har Ebone. Kamaruzzaman bai san abin da ya sa wannan al'amari ba. Tsammani ya ke yi Badura ta koma garinsu tuni.
Da isarsu suka tafi da Kamaruzzaman wajen Sarki Badura, ta duba ta ga Kamaruzzaman ne. Amma shi bai gane ta ba, don ta sha nadi, ga amawali da wando mai zina, ga alkyabba ta sa ta kame bisa karaga ana fadanci. Ta yi kamar ba ta san shi ba. Ta sa Sarkin Zagi ya ba shi daki, ya ajiye kayansa.
Dare na yi ta kira shi, ta kai shi wajen Hayatunnufusi ta cire rawani. Ko dâ ya duba sai ya gane ta. Suka rungume jana, suna kuka don murna. Hayatunnufusi ma da ba ta san shi ba, don tausayi har ta taimaka musu kuka.
Da suka share hawaye, Badura ta kwashe labarin abin da ya auku bayan rabuwarsu duk ta gaya masa, Kamaruzzaman ya dubi Hayatunnufusi, ya ce, “Allah ya yi miki albarka kin ko cika ’ya. Mun ko gode wannan asiri da kika rufa mana.” Shi kuma ya kwashe labarinsa duka ya ba su, suka sake fashewa da kuka don tausayi da murna. Cikin daren nan suka dunguma su duka uku, suka tafi wajen tsohon Hayatunnufusi, suka bayyana masa abin da ya faru duk tun farko har tarshe. Kamaruzzaman kuma ya gaya masa yadda ya auku har ya auri Badura, da yadda suka rabu. Sarki ya yi mamakin wannan abu.
Gari na wayewa aka tara mutanen gari, aka gaya musu labarin abin nan da ya faru duka, suka yi ta mamakin wannan al’amari.
Kamaruzzaman kuma ya nemi a ba shi Hayatunnufusi, Sarki ya yarda da wannan. Aka yi shagali wanda ba ya bayyanuwa cikin wannan dan lokaci. Aka yi wa Kamaruzzaman sarauta maimakon Badura, suka yi ta cin duniyarsu.
Daga
Ishaq Ibrahim shuaibu sagah

- At sunday 14 July 2019

Comments
Post a Comment