*LABARIN TANIMUDDARI*
(Namiji mai
ganin abubuwan Al'ajabi)
Watarana Manzon Allah (S.A.W) yana
zaune tare da sayyidina Ali (R.A), sai
ya hangi TANIMUDDARI yana
wucewa,, sai ya fashe da kuka.
Sayyidina Ali (R.A) yace "Ya
Rasulullulahi me ya sa ka kuka?".
Yace "Ka ga mutumin can, bayana
musiba zata afku gunsa, zai ga
abubuwan mamaki iri-iri, domin
Mala'ika Jibrilu (A.S) ya bani labarinsa
tuntuni.
Da washegari Manzon Allah yana
zaune,, sahabbansa sun kewaye shi,, ya buda baki yace "Ya ku jama'ar
musulmi ayi wanka kada a kwana da
janaba. Domin an fi son mutum ya
kwana mai tsarki".
Shi kuwa Tanimuddari yana wurin ya ji
abinda Manzon Allah(saw) ya fadi.
* *
Bayan 'yan kwanaki bayan wafatin manzon Allah (saww) Tanimuddari
janaba ta same shi ya tashi dan ya yi
wanka,, ya tafi Bandaki,,,matarsa ta kai
masa ruwa. Ya tube kayansa,, ya
tsugunna. Ashe koda ya tsugunawarsa a
bisa fiffiken wani Aljani yake,, sunansa
kuwa "IFRITU",, ga shi kuwa kafirin
'Aljani ne.
Tanimuddari ya kamfato ruwa zai zuba
a jikinsa sai yace"Bismillahi". Sai Ifritu
ya yi tsalle da shi bisa wani tsibiri a
tsakiyar "Baharul-muhid". Tsakanin
tsibirin nan da Tanimmudari zuwa
Makkah tafiyar shekara Saba'in ce.
Al'amarin cikin rabin dare na karshe
aka yi shi.
Matarsa ta jima bata ga ya dawo ba, sai
ta fito tana duddubawa gabas da
yamma,,kudu da Arewa, bata gan shi
ba,, ba ta kuma ji duriyarsa ba. Sai tayi
zaton ko watakila ya tafi masallaci dan
yayi sallah Raka'a biyu. Ta tasamma
kofar gidan,, ta tarar da kofa a kulle
kamar Da.
Sai ta buga kururuwa tace, "Kaicho ni
kaina, ina ya tafi? Sai ta koma ta ida
rurumi,,(ma'ana ta dan kwanta ta
rintsa),,,amma batun zuci ya kai ya
kawo.
Tun da sassafe ta tafi gidansu ta
shaidawa iyayenta,,ko da kuwa ita 'yar
kawunsa ce,,Auren zumunta ne aka yi
masu.
Danginta suka yi mamaki,,suka watsu
suna nemansa a cikin unguwa,,,ba su
same shi ba.
Matar ta hakura ta zauna shekaru biyu
kamilan. Da bata ji duriyarsa ba(labari),
sai ta tafi wurin Halifa,, Umaru dan
Khaddabi (R.A) tace, "Ya Amirul
muminina,, ka sani dai mijina Tanimuddari
ya bata,,na zauna yau shekara biyu
ban ganshi ba,,ban kuma ga wanda ya
ganshi ba,, in ka bani izini in yi Aure
na gode".
Halifa yace,"Kara hakuri shekaru biyu
ko Allah ya sa ya zo,, in bai zo ba, ma
samu labarinsa". Matar ba ta kauda
maganar Halifa ba,,ta koma ta yi ta
hakuri har na tsawon shekaru bakwai.
A cikin shekara ta takwas,, ta koma
wurin Halifa Umar dan Khaddabi (R.A)
tace,"Ba ka umurceni ba,,da miji?
Zama haka gobruwa bai kamata
ba,,,ina tsoron kaina kada in bata
sunana". Ita kuwa mace ce kyakkyawa,
har abada fuskarta kyalkyali ta ke
yi.
Halifa ya waiwayi sahabbai ya ce, "Me
ku ka gani?". Suka ce "Ganinka shine
na mu".
Sai Halifa yace mata,"Koma wurin
danginki,,kiyi Idda irin Iddar mamaci,,
in kin kare ki komo mani".
Yarinya ta komo Gida ta zauna wata
Hudu da kwana goma. Da ta gama
Iddarta ta koma wurin Halifa tace,"Na
kare". Sa'annan Halifa yace ma
jama'arsa,"Wa zai auri yarinyar nan"?
Daga nan wani namiji mutumin Qabilar
BANI UZRATA ya yi zumbur yace,"Ni
zan Aureta Ya Amirul Muminina".
Halifa ya daura masu Aure bisa
farillolin ubangiji da sunnonin Manzon
Allah (S.A.W).
Miji ya koma gidansa mata ta dawo
gidanta.
Gabanin Azahar Ango ya ba da
shinkafa da kudin cefane yace "A
kawo ma amarya, ta yi Abinci kafin in
zo"
Ta aika aka yo mata tarkacen kayan
miya ta dora sanwa ta yi abinci,, ta ci
nata ta ajiye ma Ango nasa.
Tun bai ida Hucewa ba sai Ango ya
danno. Da isowarsa ta dauko nasa ta
kawo masa ta girke a gabansa, ta
komo ta mika ma makota na su....
Komowar nan da take yi sai ga
Tanimuddari ya sauko daga sama. Ya
ce, "Assalamu Alaikum, ya diyar
Umaru".
Zanci gaba
Daga naku Mai debe kewa a gareku
Ishaq Ibrahim Shuaibu Sagah
(Namiji mai
ganin abubuwan Al'ajabi)
Watarana Manzon Allah (S.A.W) yana
zaune tare da sayyidina Ali (R.A), sai
ya hangi TANIMUDDARI yana
wucewa,, sai ya fashe da kuka.
Sayyidina Ali (R.A) yace "Ya
Rasulullulahi me ya sa ka kuka?".
Yace "Ka ga mutumin can, bayana
musiba zata afku gunsa, zai ga
abubuwan mamaki iri-iri, domin
Mala'ika Jibrilu (A.S) ya bani labarinsa
tuntuni.
Da washegari Manzon Allah yana
zaune,, sahabbansa sun kewaye shi,, ya buda baki yace "Ya ku jama'ar
musulmi ayi wanka kada a kwana da
janaba. Domin an fi son mutum ya
kwana mai tsarki".
Shi kuwa Tanimuddari yana wurin ya ji
abinda Manzon Allah(saw) ya fadi.
* *
Bayan 'yan kwanaki bayan wafatin manzon Allah (saww) Tanimuddari
janaba ta same shi ya tashi dan ya yi
wanka,, ya tafi Bandaki,,,matarsa ta kai
masa ruwa. Ya tube kayansa,, ya
tsugunna. Ashe koda ya tsugunawarsa a
bisa fiffiken wani Aljani yake,, sunansa
kuwa "IFRITU",, ga shi kuwa kafirin
'Aljani ne.
Tanimuddari ya kamfato ruwa zai zuba
a jikinsa sai yace"Bismillahi". Sai Ifritu
ya yi tsalle da shi bisa wani tsibiri a
tsakiyar "Baharul-muhid". Tsakanin
tsibirin nan da Tanimmudari zuwa
Makkah tafiyar shekara Saba'in ce.
Al'amarin cikin rabin dare na karshe
aka yi shi.
Matarsa ta jima bata ga ya dawo ba, sai
ta fito tana duddubawa gabas da
yamma,,kudu da Arewa, bata gan shi
ba,, ba ta kuma ji duriyarsa ba. Sai tayi
zaton ko watakila ya tafi masallaci dan
yayi sallah Raka'a biyu. Ta tasamma
kofar gidan,, ta tarar da kofa a kulle
kamar Da.
Sai ta buga kururuwa tace, "Kaicho ni
kaina, ina ya tafi? Sai ta koma ta ida
rurumi,,(ma'ana ta dan kwanta ta
rintsa),,,amma batun zuci ya kai ya
kawo.
Tun da sassafe ta tafi gidansu ta
shaidawa iyayenta,,ko da kuwa ita 'yar
kawunsa ce,,Auren zumunta ne aka yi
masu.
Danginta suka yi mamaki,,suka watsu
suna nemansa a cikin unguwa,,,ba su
same shi ba.
Matar ta hakura ta zauna shekaru biyu
kamilan. Da bata ji duriyarsa ba(labari),
sai ta tafi wurin Halifa,, Umaru dan
Khaddabi (R.A) tace, "Ya Amirul
muminina,, ka sani dai mijina Tanimuddari
ya bata,,na zauna yau shekara biyu
ban ganshi ba,,ban kuma ga wanda ya
ganshi ba,, in ka bani izini in yi Aure
na gode".
Halifa yace,"Kara hakuri shekaru biyu
ko Allah ya sa ya zo,, in bai zo ba, ma
samu labarinsa". Matar ba ta kauda
maganar Halifa ba,,ta koma ta yi ta
hakuri har na tsawon shekaru bakwai.
A cikin shekara ta takwas,, ta koma
wurin Halifa Umar dan Khaddabi (R.A)
tace,"Ba ka umurceni ba,,da miji?
Zama haka gobruwa bai kamata
ba,,,ina tsoron kaina kada in bata
sunana". Ita kuwa mace ce kyakkyawa,
har abada fuskarta kyalkyali ta ke
yi.
Halifa ya waiwayi sahabbai ya ce, "Me
ku ka gani?". Suka ce "Ganinka shine
na mu".
Sai Halifa yace mata,"Koma wurin
danginki,,kiyi Idda irin Iddar mamaci,,
in kin kare ki komo mani".
Yarinya ta komo Gida ta zauna wata
Hudu da kwana goma. Da ta gama
Iddarta ta koma wurin Halifa tace,"Na
kare". Sa'annan Halifa yace ma
jama'arsa,"Wa zai auri yarinyar nan"?
Daga nan wani namiji mutumin Qabilar
BANI UZRATA ya yi zumbur yace,"Ni
zan Aureta Ya Amirul Muminina".
Halifa ya daura masu Aure bisa
farillolin ubangiji da sunnonin Manzon
Allah (S.A.W).
Miji ya koma gidansa mata ta dawo
gidanta.
Gabanin Azahar Ango ya ba da
shinkafa da kudin cefane yace "A
kawo ma amarya, ta yi Abinci kafin in
zo"
Ta aika aka yo mata tarkacen kayan
miya ta dora sanwa ta yi abinci,, ta ci
nata ta ajiye ma Ango nasa.
Tun bai ida Hucewa ba sai Ango ya
danno. Da isowarsa ta dauko nasa ta
kawo masa ta girke a gabansa, ta
komo ta mika ma makota na su....
Komowar nan da take yi sai ga
Tanimuddari ya sauko daga sama. Ya
ce, "Assalamu Alaikum, ya diyar
Umaru".
Zanci gaba
Daga naku Mai debe kewa a gareku
Ishaq Ibrahim Shuaibu Sagah
Comments
Post a Comment